Home Back

"Ina Dai Lafiya Kam": Atiku Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Zame Har Kasa a Faifan Bidiyo

legit.ng 2024/7/1
  • Yayin da ake ta yaɗa faifan bidiyon Shugaba Tinubu lokacin da ya zame a Eagle Square, Atiku Abubakar ya yi martani
  • Ɗan takarar shugaban kasa PDP ya nuna damuwa da alhini kan abin da ya faru da shugaban a yau Laraba 12 ga watan Yuni
  • Atiku ya wallafa haka ne a shafinsa na X inda ya jajantawa Tinubu tare da fatan yana cikin koshin lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya magantu bayan Bola Tinubu ya zame yayin bikin dimukradiyya.

Atiku ya jajantawa Tinubu dangane da zamewar inda ya ce yana fatan shugaban yana cikin koshin lafiya.

Atiku ya magantu bayan Tinubu ya zame a taro
Atiku ya jajantawa Tinubu bayan zamewa a taron dimukradiyya. Hoto: Sean Gallup/Kola Sulaimon. Asali: Getty Images

Atiku ya jajantawa Tinubu bayan ya zame

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka a shafinsa na X da bidiyon abin da ya faru a yau Laraba 12 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina jajantawa Shugaba Tinubu dangane da hatsarin da ya afku da shi yayin da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya.
"Ina dai fatan yana lafiya, babu wata matsala."

- Atiku Abubakar

Dimukradiyya: Tinubu ya zame a taro

Wannan na zuwa ne bayan an yaɗa wani faifan bidiyo da shugaban ya zame yayin da yake hawa matakalar mota yayin bikin.

An gudanar da bikin ne a dandalin 'Eagle Square' da ke birnin Abuja domin murnan ranar dimukradiyya a Najeriya.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading