"Ina Dai Lafiya Kam": Atiku Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Zame Har Kasa a Faifan Bidiyo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya magantu bayan Bola Tinubu ya zame yayin bikin dimukradiyya.
Atiku ya jajantawa Tinubu dangane da zamewar inda ya ce yana fatan shugaban yana cikin koshin lafiya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka a shafinsa na X da bidiyon abin da ya faru a yau Laraba 12 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina jajantawa Shugaba Tinubu dangane da hatsarin da ya afku da shi yayin da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya.
"Ina dai fatan yana lafiya, babu wata matsala."
- Atiku Abubakar
Wannan na zuwa ne bayan an yaɗa wani faifan bidiyo da shugaban ya zame yayin da yake hawa matakalar mota yayin bikin.
An gudanar da bikin ne a dandalin 'Eagle Square' da ke birnin Abuja domin murnan ranar dimukradiyya a Najeriya.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng