Home Back

Jigon APC Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Kano Ta Yi Ganduje Illa a Siyasance

legit.ng 2024/5/17
  • Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa (Arewa ta Yamma) Salihu Lukman, ya yi magana kan dambarwar ƙoƙarin tsige Abdullahi Umar Ganduje
  • Salihu ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta yi nasarar yi wa Ganduje illa a siyasance ne saboda ya kwashe na hannun damansa zuwa Abuja
  • Ya yi nuni da cewa dole a sanya alamar tambaya kan ko shugaban na APC yana son ganin jihar Kano ta sake dawowa hannun jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman, ya ɗora alhakin ƙoƙarin tsige Abdullahi Umar Ganduje, a kan rashin kula da siyasar Kano da ya yi.

Salihu Lukman ya bayyana cewa da Ganduje ya riƙe ƴan siyasar APC a Kano da kyau, da ba a yi nasarar ƙulla masa tuggun neman tsige shi ba.

Jigon APC ya fadi kuskuren Ganduje
Salihu Lukman ya fadi dalilin nasarar gwamnatin Kano kan Ganduje Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr. Abdullahi Umar Ganduje - OFR Asali: Facebook

Meyasa aka yi nasara kan Ganduje?

Salihu wanda tsohon mataimakin shugaban APC ne ya ce dalilin da ya sa gwamnatin Kano da magoya bayan NNPP suka yi nasarar yi wa Ganduje illa a siyasance, shi ne ya tattara na hannun damansa ya bar jihar bayan ya zama shugaban APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa yadda Ganduje ya yi riƙon sakainar kashi da lamuran siyasar Kano, ya sanya ayar tambaya kan ko yana da sha'awar ganin jam'iyyar APC ta dawo kan madafun ikon jihar, cewar rahoton jaridar The Guardian.

Jaridar The Punch ta ce jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

"Baya ga haka, Ganduje na zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, kusan dukkanin shugabannin APC na jihar Kano sun koma Abuja."
"Daga cikin dalilin da ya sa gwamnatin jihar Kano ta yi nasarar yi wa Ganduje illa a siyasance shi ne saboda kusan dukkanin shugabannin APC sun bar Kano."
"Maganar gaskiya tun hawan Ganduje a matsayin shugaban APC kusan watanni tara bai kai ziyara jihar Kano fiye da sau biyu ba."

- Salihu Lukman

Batun dakatar da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar APC.

Ganduje ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai damu da dakatarwar da aka yi masa ba wacce ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙullawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading