Home Back

Jami’an tsaro sun hana duk wani nau’ikan hawa a lokacin babbar Sallah, a Kano.

dalafmkano.com 2024/7/1

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta hana duk wani nau’ikan hawa, da bukukuwan babbar Sallah, da ke ƙara gabatowa, a wani ɓangare na magance matsalar tsaro a faɗin jihar Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikewa Dala FM Kano, a ranar Alhamis, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro yayin da bayan bukukuwan babbar sallar a faɗin jihar Kano.

“Daga cikin bukukuwan da aka hana akwai dukkanin hawan Sallah, ciki har da hawan Daba biyo bayan rahotanni a aka samu akan abinda ya shafi tsaro, da kuma ganawa da akayi da dukkanin masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro, “in ji Kiyawa”.

Rundunar ƴan sandan ya Kano, ta kuma ce yanzu haka ta shirya tsaf, domin samar da tsaro a faɗin jihar, kuma ba zata lamunci duk wani nau’in tayar da hankalin al’umma ba.

Har ila yau, SP Kiyawa, ya kuma ce ana kira ga al’umma kan duk wani baƙon al’amari da suka ga ya faru da su yi hanzarin sanar da jami’an su mafi kusa, ko kuma a kira waɗannan lambobi 08032419754 ko kuma 08123821575, ko 09029292926, domin ɗaukar mataki a cikin gaggawa.

Rundunar ƴan sandan ta jihar Kano, ta kuma bukaci haɗin kan al’ummar jihar baki ɗaya, domin bada gudunmawar su wajen ganin an gudanar da bukukuwa cikin lafiya da kwanciyar hankali.

People are also reading