Matashin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta, Iyayensa Sun Magantu
Bauchi - Aminu Muhammad, matashin da ya zolaya Aisha Buhari a soshiyal midiya, an sako shi daga gidan yari bayan Uwargidan shugaban kasan ta janye karar da ta kai tashi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Muhammad wanda dalibi ne a jami’ar tarayya dake Dutse, ya wallafa hoton uwargidan shugaban kasan inda yace ta ci kudin talakawa tayi kiba, wanda hakan yasa aka kama shi.
Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama
An gurfanar dashi a ranar Talata kuma aka aike shi gidan kurkukun Suleja dake jihar Niger.
Iyayen Aminu Muhammad sun bayyana jin dadinsu kan sakinsa da aka yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kawunsa, Shehu Baba Azare, wanda yayi magana a madadin iyalan, yace:
“Aminu a halin yanzu yana jami’ar tarayya dake Dutse saboda jarabawarsa kuma muna farin ciki da sakinsa.”
Ya kara da cewa:
“An saki Aminu a ranar Juma’a kuma mun jira shi saboda mun gano cewa zai gana da shugaban kasa a fadarsa daren Juma’a amma aka dage zuwa safiyar Asabar wanda ba a samu ganawar ba.
“A karshen komai, sun gana da Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, wanda ya samar masa jirgi tun daga Abuja har Dutse dake jihar Jigawa inda abokai da masoyansa suka tare shi.”
Lauya Ya Fadi Dalili 1 da ya sa ‘Yan Sanda Janye Karar Mai 'Cin Mutuncin' Aisha Buhari
“Dukkan ‘yan uwa muna matukar farin ciki da sakinsa saboda muna ta gwargwarmayar neman yancinsa na tsawon lokaci.
“Da farko mun ji cewa ba zamu iya ba har sai da muka saka jama’a inda muka samu taimakon mutane, jaridu, kungiyoyi daga ko ina. A karshe an sako Aminu.”
- Yace.
Yace an kai Aminu makaranta ta yadda zai samu damar fara shirin jarabawa wacce za a fara ranar Litinin, inda yace har yanzu basu riga da sun gan shi ba.
A wani labari na daban, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta janye karar dalibin da ya caccaketa tare da cewa taci kudin talakawa tayi kiba.
Lauyan dalibin, C. K Agu ya tabbatar da hakan a Abuja da yammacin Juma’a.
Asali: Legit.ng