Home Back

'Ga ni da kuɗi a asusuna, amma burodi ya fi karfina'

bbc.com 2024/7/1

Asalin hoton, Getty Images

Gaza
Bayanan hoto, Na'urorin ATM da dama ba sa aiki an lalatasu a Gaza
  • Marubuci, Amira Mhadhbi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic

"Akwai kwanakin da ba na iya saya wa yarana burodi, duk da cewa akwai burodin kuma ina da kuɗin saye a bankuna."

Mohamed al-Kloub, Bafalasɗine daga Deir al Balah a Gaza, ya ce kuɗin da ke asusunsa na banki ba su da amfani muddin ba zai iya ciresu ba, inda 'yan kasuwa da dama ba sa karba ko yarda da tsarin tura kuɗi a asusun banki.

Ana cikin yanayi na ƙarancin kuɗi sosai a Gaza a watannin baya-bayanan, musamman bayan sojojin Isra'ila sun datse kuɗaɗen harajin da ake bai wa Falasɗinawa a Gaza.

Matsalar Kuɗi

A watannin farko na soma yaƙi a Gaza, yayin da alkaluman mutanen da aka raba da matsugunai ke karuwa, 'yan Gaza sun yi dogayen layuka a gaban naurar cire kuɗi na ATM, suna dafifin cirar kuɗi.

Wasu sun tsaya na tsawon kwanaki kafin layi ya zo kansu.

Yayin da lokaci ke kara ja, ana samun ƙarin bankunan da ake ruguzawa a yaƙin, wasu fararen-hula sun kafa daba ta masu harkar canji" - sun kasance masu samar da kuɗin da kuma haifar da wahalarsa.

A ranar 24 ga watan Maris, wata shida bayan soma yakin, Hukumar kula da hada-hadar kuɗi ta Falasɗinawa ta ce zai yi wahala ta samar da wasu rassanta a yankunan Gaza saboda ci gaba da kai harin bama-bamai, ƙarancin lantarki da kuma hali na hakika da ake ciki.

Wannan na sake haifar da tsananin wahala na kuɗi, inda galibin na'urorin ATM ba sa aiki.

A ranar 11 ga watan Mayu, hukumar kula da harkokin kuɗi ta Falasɗinawa ta kaddamar da tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta intanet, ta hanyar manhajoji da katin banki.

Sai dai, rashin intanet ya zama babban kalubale - kuma hakan na sake zama barazanar da ake sabawa da ita.

"A watanni takwas na wannan yaƙi, shago ɗaya kawai na samu da ke karban kuɗi ta hanyar turawa a banki - musamman a wannan lokaci da ake sayar da kayayyaki a tantunan 'yan gudun hijira maimakon shaguna," a cewar Mohamed.

Asalin hoton, Getty Images

Yadda 'yan Gaza ke shafe kwanaki a kan dogon-layi wajen cirar kudi a ATM
Bayanan hoto, Yadda 'yan Gaza ke shafe kwanaki a kan dogon-layi wajen cirar kuɗi a ATM

Tattalin arzikin Gaza

Domin fahimtar abin da ke sake haifar da karancin kuɗi a Gaza, dole sai mutum ya fahimci abin da ke haifar da wannan matsala a zirin.

Tattalin arzikin Gaza ya fuskanci durkushewa saboda takunkumin da aka kakaba musu bayan Hamas ta kwace ikon yankin a 2007.

Isra'ila ta ce sanya takunkumin na da muhimmanci domin hana hare-haren mayakan.

Bankuna a zirin Gaza na da alaka da hukumar da ke sa ido kan kuɗaɗe a Gaza da kuma gwamnatin Falasɗinawa ta Ramallah, ko kuma kamfanoni masu zaman kansu da ke da alaka da Hamas.

An kafa Hukumar da ke kula da harkokin kuɗi a 1994 karkashin yarjejeniyar da aka cimma a Paris, kuma wani ɓangare ne na bunƙasar tattalin arziki bisa tsarin yarjejeniyar Oslo.

Waɗannan yarjeniyoyi sun bai wa Isra'ila damar sa ido da iko da tattalin arzikin Falasɗinu.

Karkashin tsarin, Isra'ila na karban haraji daga Falasɗinawa sannan su aika kuɗin, a kowanne wata, zuwa ga asusun bai-ɗaya - bayan amincewa da sa hannun ma'aikatar kuɗi ta Isra'ila, da kuma cire kuɗin ruwa.

Waɗannan kuɗaɗe, da ake bayyana su da kuɗaɗen haraji, su ne babban hanyar samar da kuɗin shiga ga Falasɗinawa, wanda kuma ciki ake ware wa Gaza.

Lokacin da Hamas ta kwace ikon zirin Gaza a 2007, dubban fararen-hula a Gaza da ke aiki sun ci gaba da samun albashinsu daga hukumomin Falasɗinawa.

Kuɗaɗen na zuwa daga Gaza daga tallafin da ake samu daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasɗinawa a Majalaisar Ɗinkin Duniya, UNRWA, da Qatar da suke samar da kusan duk dalolin da ake gani a Gaza.

Mai bincike ta fannin tattalin arziki a Gaza, Ahmed Abu Qamar, ya bayyana wannan a matsayin hanyar rayuwa da samar da kuɗi a hukumance.

Ya kuma faɗa wa BBC cewa akwai wasu hanyoyin bayan fagge, inda mutane ke mayar da wasu abubuwa na amfani kuɗi.

Amma kuɗaɗen da ake samarwa ta wannan hanya ba sa cikin lissafi ko bayanan kuɗaɗen yankin, a cewarsa.

Ya jadadda cewa kuɗaɗen da ake samu a yankin Gaza sun isa wajen gina ƙasar da inganta rayuwar al'ummar ƙasar sama da miliyan biyu da ke rayuwa a zirin.

Kuɗaɗen da ake amfani da su a hada-hada;

  • Kuɗin shekel na Isra'ila: shi ne fitaccen takardan kuɗi da ake rayuwa da shi a siyayyar yau da kullum
  • Dalar Amurka: da shi ake amfani wajen shigo da kayayyaki, cinikaya tsakanin kasa da kasa da kuma sayen manyan kadarori irin su motoci.
  • Kuɗin dinar na Jordan: bisa al'ada ta shi ake biyan sadakin aure, sayen filaye da kadarori, biyan kuɗin makaranta da sauransu.

Asalin hoton, Getty Images

Gaza
Bayanan hoto, Kuɗin shekel na Israila na cikin kuɗaɗen da aka fi kashe wa a Gaza

Tasirin yakin

Tun soma wannan yaki, mahukuntan Isra'ila suka daina aika kuɗaɗen haraji da kuɗaɗen da ake bai wa zirin Gaza a asusun hukumar hada-hadar kuɗi ta Falasɗinu.

Isra'ila na cewa kuɗin na taimakawa wajen ƙara wa Hamas karfi.

A watan Nuwamban 2023, ma'aikatar kuɗi ta Falasɗinu ta sanar da cewa ministan harkokin kuɗin Isra'ila ta zabtare musu miliyan 600 daga kuɗaɗen haraji kowanne wata da suka haɗa da kuɗin biyan albashi, alawus na ma'aikata da sauran kuɗaɗen yankin na Gaza."

A farkon wannan shekarar, Ministan harkokin kuɗin Isra'ila Bezalel Smotrich ya yi barazanar hana mahukuntan Falasɗinu dukkanin kuɗaɗensu na haraji muddin sisin kwabonsu ya shiga Gaza.

Kasuwar bayan-fagge

Shaguna sun lika sanarwa cewa sun daina bada kudi
Bayanan hoto, Shaguna sun lika sanarwa cewa sun daina ba da kuɗi

An tilasta wa Mohamed al- Kloub dogaro da kasuwannin bayan-fagge, inda yake samun kuɗaɗe daga wani shago, tare da ba da kwamisho daga tsakanin kashi 10 zuwa 20 cikin 100, sai dai wannan hanyar ma da ake lallaɓawa na neman gagararsa a cewar Mahmoud Bakr al-Louh.

Shagunan da a baya ake samun kuɗaɗe a yanzu suna makale cewa babu kudin ko da za ka ba da kwamisho. A yanzu abin ya koma sai wanda ka sani, a cewar Mahmoud.

Ahmed (ba sunansa na gaskiya ba) ya yi wa BBC bayani kan tsarin kudaden kwamisho da suke karɓa daga masu neman tsabar kuɗi.

Ya soma shirin biyan diyya ga shi kansa asarar da ya tafka lokacin cirar kudi har dubu 40 daga asusunsa.

Ya ce dole ya biya kashi 10 cikin 100 na kwamisho. Yanzu Ahmed ya biya kashi 13 cikin 100 na kudaden da yake bai wa kwastamomi.

Ribar da yake samu bai taka kara ya karya ba. Amma dole al'ummar Gaza su ci gaba da lallaɓawa da neman wasu hanyoyin rage raɗaɗin da suke fama da shi a kullum.

People are also reading