Home Back

Gwamnatin Buhari Ta Ci Bashin N30tr a CBN? Gaskiya Ta Bayyana

legit.ng 6 days ago
  • An gano adadin kuɗaɗen bashiin 'Ways and Means' da gwamnatin tarayya ta karɓa daga wajen babban bankin Najeriya (CBN)
  • Wasu takardu da aka gani sun nuna cewa gwamnatin ta karɓi N7.5tr ne saɓanin N30tr da aka ta karɓa a wajen bankin na CBN
  • A kwanakin baya dai majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki yadda aka yi amfani da kuɗaɗen waɗanda aka karɓo daga CBN

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bashin 'Ways and Means' da bankin CBN ya ba gwamnatin tarayya a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari na ci gaba da tayar da ƙura.

Bayanan da suka fito kwanan nan sun nuna cewa adadin yawan kudaɗen su ne N7.5trn ya zuwa watan Disamban 2022.

Gwamnatin Buhari ta ci bashi a hannun CBN
Gwamnatin Buhari ba ta ci bashin N30tr a hannun CBN ba Hoto: @BuhariSallau1, @cenbank Asali: Twitter

Jaridar TheCable ta ce takardun da ta gani sun nuna cewa adadin kuɗaɗen shi ne N7.5tr saɓanin N30tr da kwamitin majalisar dattawa ya ce su ne kuɗaɗen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa dai ta kafa kwamitin ne domin binciken yadda aka yi da kuɗaɗen wanda CBN ya ba gwamnatin tarayya.

Adadin bashin da aka biyo gwamnati a CBN

Takardun da jaridar TheCable ta gani sun nuna cewa ya zuwa ranar, 19 ga watan Disamba 2022, adadin bashin da ke asusun gwamnatin tarayya na CBN shi ne N22,719,703,774,306.90.

Wannan adadin ya haɗa da N7,531,819,048,929.66 a matsayin bashin 'Ways and means', N13,725,408,432,557.50 a matsayin jimillar kuɗaɗen hada-hadar gwamnati a kasuwar hannun jari, sai N4,618,829,652,047.41 a matsayin kuɗin ruwa.

Basussukan ba a sanya su cikin waɗanda ake bin gwamnatin tarayya ba har sai watan Disamban 2022 lokacin da gwamnatin Buhari ta buƙaci majalisar tarayya ta yi hakan.

Sau nawa Buhari ya ciyo bashin a CBN

Sau uku ne kawai a lokacin mulkin Buhari ya nemi bashin 'Ways and Means' duk da dai an ba da kuɗaɗen fiye da sau uku.

Adadi mafi girma wanda ya kusa N2tr an ba da shi ne a lokacin annobar cutar korona sakamakon rage samun kuɗaɗen shiga da gwamnati ta yi.

Adadi mafi girma na biyu da aka ba da, an ba da shi ne a shekarar 2022 inda aka ba gwamnatin tarayya N1,473,618,756,185.62.

A shekarar 2019, lokacin da Buhari ya yi tazarce, an ba gwamnatin tarayya N1.4tr.

CBN ya daina ba gwamnati bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu ya daina bayar da bashin 'Ways and Means' ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ya dauki matakin ne saboda gazawar gwamnati wajen biyan basussukan da ake bin ta.

Asali: Legit.ng

People are also reading