Home Back

Hadaddiyar Daular Larabawa Za Ta Fara Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza – Gwamnatin Tarayya

leadership.ng 2024/7/2
Hadaddiyar Daular Larabawa Za Ta Fara Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza – Gwamnatin Tarayya

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana shirin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, na dage haramcin bayar da izinin shiga kasar ga matafiyan Nijeriya, nan ba da jimawa ba.

Keyamo, yayin wata ganawa da babban hadimin Shugaban Kasa Bola Tinubu, Otega Ogra, wacce aka wallafa a shafin fadar shugaban kasa na YouTube, ya ce an riga an cimma yarjejeniya tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan a ziyarar da Tinubu ya kai kasar a watan Satumbar bara.

A cewarsa, duk da cewar Hadaddiyar Daular Larabawan ta zayyana karin ka’idojin da za a cika kafin a dage haramcin a hukumance, tuni gwamnatin tarayya ta kammala cika su, abin da ya share hanyar jiran sanarwa daga gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawan.

Keyamo ya kara da cewar, “Bayan ganawar shugabanin kasar, Shugaba Tinubu ya saukaka mana aiki, inda muka yi ta bibiya a matsayinmu na ministocinsa. Mun yi duk abin da ya kamata. Mun warware komai. Yanzu saura a jira sanarwar daga hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawan. Wacce tabbas tana tafe.”

Keyamo ya ci gaba da cewar, ya san ranar da za a dage haramcin bayar da bizar, sai dai ya jaddada cewar ganin damar gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawan ne ta fitar da sanarwa a hukumance.

Ana sa ran dage haramcin ya dawo da saukin yin balaguro ga ‘yan Nijeriya da ke zuwa Dubai, kuma hakan zai inganta alaka da hadin kai tsakanin kasashen biyu.

People are also reading