Home Back

Tsadar Rayuwa Ba Zai Sa Tinubu Ya Yi Murabus Ba: Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Gwamnonin PDP

leadership.ng 2024/4/28
Dalilin Kotu Na Dakatar Da Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Tinubu

Gwamnatin tarayya ta yi zazzafar martani ga gwamnonin jam’iyyar PDP, inda ta bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai yi murabus  daga shugabancin Nijeriya ba sakamakon tsadar rayuwa da ake ciki.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ba zai yi murabus ba saboda halin da tattalin arziki ke ciki.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rabiu Ibrahim, ya fitar lokacin da yake mayar da martani ga gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP kan kiran shugaban kasa ya yi murabus saboda tsadar rayuwa da ke fama da ita a kasar nan.

A cawarsa, kiran da gwamnonin jam’iyyar adawan ke yi ba wani abu ba ne illa fusata mutane wadanda suke biyayya ga shugaban kasa wajen kokarinsa na kawo sauki ga al’ummar Nijeriya.

Ya ce jam’iyyar PDP da gwamnoninta bai kamata su biyo ta bayan fage wajen sukar gwamnati ba, domin sun gaza cimma irin wannan kokarin lokacin da suke rike da jan ragamar shugabancin Nijeriya har zuwa 2015.

“Wadanda suka kasa kawo sauyi lokacin da suke da dama, bai kamata su dunga janye hankalin mutane wajen sukar shugaban da ke da muradin kawo sauyi da ‘yan Nijeriya suka zaba ba.

“Tun farkon wannan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayar da kudade ga gwamnatocin jihoji ba tare da nuna wani bambancin jam’iyyar ba. Bugu da kari, cire tallafin man fetur yana daga cikin manyan abubuwan da dan takarar shugaban kasa na PDP ya ayyana a lokacin yakin neman zabe a matsayin wata hanyar da zai samar wa dukkan jihohi kudaden shiga. Saboda haka wannan ba abun suka ba ne,” in ji Idris.

Idris ya ce shugaban kasa yana aiki tukuru wajen farfado da tattalin arziki ta hanyar wasu shirye-shirye da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara na inganta ababen more rayuwa, tallafa wa al’umma, samar da kayayyakin aiki da kulawa da jin dadin jami’an tsaro da kuma sake dawo da Nijeriya cikin hayyacinta.

Ya nanata cewa ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa da gwamnatin APC ba, saboda ita ce ta biya wasu basuka da gwamnatin PDP ta ciyo domin biyan kudin tallafi da kasa biyan kudaden fansho da albashin ma’aikata.

Ya kuma ce an gyara manyan bangarori na man fetur da PDP ta gaza gyarawa shekaru da dama tare da gina sabbin matatan mai da kuma sauran ayyukan ci gaba da APC take shimfidawa a Nijeriya.

 
People are also reading