Home Back

Fargabar tayar da bama-bamai a majalisar dokokin Kano: Har yanzu ƴan majalisa ba su koma aiki ba

premiumtimesng.com 3 days ago
Kano State Assembly
Kano State Assembly

Makonni uku kenan da kammala hutun ƴan majalisar dokokin jihar Kano, sai dai kuma komawa majalisar ya gagare su saboda fargabar tayar bama-bamai da ake zargin wasu za su yi a harabar zauren Majalisar.

Majiyoyi sun ce tsaikon da aka samu ya biyo bayan gargadin da ‘yan sandan suka yi na wani shiri da wasu batagari suka yi na tada bama-bamai a harabar majalisar.

Ana jingina wannan batu da rusa masarautu da gwamnatin Kano ta yi da tun bayan haka ake ta kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Kano da hukuncin kotu game da rusa masarautun da kuma dawo da Sarki Sanusi kan karagar mulkin Kano.

Ƴan majalisar ba su dawo daga hutu ba saboda fargabar kada Bom ya tashi da suna aiki.

A ranar 26 ga watan Mayu ne tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya ce jami’an tsaro sun samu rahoton sirri cewa wasu ƴan ta’adda na shirin tayar da bam a harabar majalisar.

“Wasu na kokarin ganin sun haifar da rashin zaman lafiya Kano ta hanyar kai hare-hare a wurare, musamman majalisar dokoki, da kuma wasu fitattun wurare a cikin babban birnin jihar. Majiya da dama sun tabbatar da wannan rahoton na leken asiri.

” A dalilin haka muna gargaɗin mutane da wanda ya ke ganin shi shafaffe da mai ne ya fito ya tsakale mu, za mu nuna masa ruwa ba tsarar kwando bane.” In ji Gumel

People are also reading