Home Back

Huawei Zai Tallafa Wa Ci Gaban Fasahar Nijeriya Ta Hanyar Zuba Dala Miliyan 15 Duk Shekara

leadership.ng 2024/6/26
Huawei Zai Tallafa Wa Ci Gaban Fasahar Nijeriya Ta Hanyar Zuba Dala Miliyan 15 Duk Shekara

Huawei Technologies ya sha alwashin bunkasa cigaban fasahar zamani, duk da cewa ta sanar da shirinta na karfafa guiwar abokan hulda ta hanyar zuba hannun jarin dala miliyan 15 a kowace shekara.

Wannan wani mataki ne na dabarbarun Huawei wajen ganin ta habaka dangantarta da abokan hulda, don bai wa kwastomomi damar samun kima mai daraja ta hanyar sauyin da fasahar zamani ya kawo wa duniya.

A yayin taron Huawei Nigeria Connect 2024, da ya gudana a karshen mako a Legas, wanda ya hada fuskokin abokan jere wajen ganin sun tattauna hanyoyin da suka jibinci cin gajiyar fasahar sadarwar zamani (ICT), cigaban masana’antu, da sabbin dabarun cigaban kamfanoni wajen ganin an kyautata cinikayya.

Manajan gudanarwa na rukunin kasuwanci na Huawei Nigeria, Terrens Wu, ya nuna godiya da irin goyan baya da suke samu daga wajen kwastomominsu masu daraja da abokan hulda wajen isar da fasahohin zamani lungu da sako.

A cewar Wu, fasaha ta bayar da dama ga abubuwa da daman gaske, kuma, “Muna rungumar sabbin fasahohi da suka hada har da fasahar kwakwalwa da fasahar zamani a Nijeriya.”

“Yanzu haka, kowa da kowace kungiya da kuma kowace kasa kowa na magana kan tattalin arzikin fasahar zamani, musamman ganin yadda fasaha ke cigaba, cikin sauki za mu samu hanyoyin habaka tattalin arzikin fasahar zamani.

Ya ninka sau biyu na kayan da kasashe ke fitarwa (GDP) a wasu kasashe da dama.

“Don haka ina gaya mana muddin kamfani da kasashe za su rungumi sauyin fasahar zamani kuma su yi amfani da shi, tattalin arziki cikin sauki zai karu za a samu bunkasar abubuwan da kasashen ke fitarwa (GDP).”

Wu ya lura da cigaban da ma’aikatu da rassan gwamnati ke samu a Nijeriya musamman ma’aikatar kirkire-kirkiren sadarwa da tattalin arzikin zamani, kamar yadda kasar ke da burin kawar da iskar carbon a nan da zuwa 2050, lamarin da ke da bukatar muhimman maida hankali da gudunmawa.

Ya sanar da cewa, Huawei, “Akwai rukunin sola guda 100 na Huawei a Nijeriya da ke da karfin sama da MW 30.

“Domin cimma sauyin fasahar zamani, komai ya tafi yadda ya dace, mun karfafa manyan kasuwancinmu guda 6 domin bunkasa karfinmu da hidimar masana’antu daban-daban. Ba kawai zallar wannan ba, zuwa yanzu, muna da hannu sosai a harkar sadarwa, harkar sadarwa ta wayar salulu na 4G wanda ta kai kashi 84 cikin 100 a Nijeriya. A bangaren kirkirarriyar fasaha ta (AI), kashi 40 na masa’antu sun rungumi ayyukan Huawei wanda ke nuni da cewa ayyukan na tasiri da fa’ida sosai a duniyar fasahar zamani.”

Ya yi fatan cewa, abokan jerensu za su hada karfi da karfe da Huawei wajen ganin dabarbatun da suke da sun kai ga taimakon kasashe da daman gaske wajen cimma nasara a bangaren sauyin fasaha, “Muna ganin yadda ake zuba hannun jari kuma hakan ke cigaba da wakana a bangaren fahar zamani da cigaban kwakwala.”

Ya nanata cewa za su cigaba za su cigaba da duba hanyoyin taimaka wa cigaban fasahar Nijeriya da kyautata alakarsu da yayi kyau na tsawon shekara 25.

A cewarsa, a tsakanin 2018 zuwa 2023, Huawei ta horas da ‘yan Nijeriya sama da 50,000 a bangaren ICT, da wasu kamfanonin Nijeriya sama da 200 da suka samu shaidar hulda da Huawei. Ya ce, Huawei ya kuma gina cibiyoyin gudanar da ayyuka na shiyya guda 10 (RNOC) a Nijeriya da ke kula da kasashe 12 da suka hada da Nijeriya Botswana, Ghana, Sierra Leone, South Africa, Comoros, Mauritius, Tanzania, Zambia, and Somalia.

People are also reading