Home Back

AIKI SAI MAI SHI: Sojoji sun lallasa ɗaruruwan ƴan bindiga, sun yi kame har da jirgin sama, jiragen ruwa, bindigogi da bamabamai

premiumtimesng.com 2024/9/27
GABA DAI SOJOJIN NAJERIYA: Yadda dakarun ‘Operation Haɗin Kai’ su ka murƙushen harin ‘yan ta’adda kan tubabbun Boko Haram

Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa a cikin makon jiya dakarunta sun kashe Ƴan ta’adda 227, sun kama wasu 529 sannan sun ceto mutum 253 da maharan suka yi garkuwa da su a faɗin kasar nan.

Jami’in yada labarai na hukumar Edward Buba ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.

Buba ya ce a wannan mako dakaru sun kwato bindigogi 231, harsasai 6,441, jirgin sama kiran ‘Eastern Bloc’ daya da tankan yaki kirar ‘MRAP’ daya.

A Arewa maso Gabashin Najeriya, Buba ya ce dakarun ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe mahara 83, sun kamo wasu 59 sannan sun ceto mutum 58 da makamai da dama.

Ya ce ‘yan ta’adda 219 sun mika wuya daga ranar 8 zuwa 14 ga Mayu da suka haɗa da maza 29, mata 65 da yara kanana 125.

A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven da ‘Whirl Stroke’ sun kashe mahara 27 sun kama wasu 154 sannan sun ceto mutum 42 da aka yi garkuwa da su.

A Arewa ta Yamma rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan bindiga 58, sun kama wasu 125 sannan sun ceto mutum 105 da aka yi garkuwa da su.

A ranar 8 ga Mayu dakarun rundunar sojin sama sun Yi wa maboyar mahara ruwan bama-bamai a Faskari dake jihar Katsina.

Dakarun sun kai wannan hari bayan sun samu bayanan sirri game da maboyar sannan a harin jami’an tsaron sun ragargaza gidajen, motoci da sauran kayan aikin maharan.

Buba ya ce rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun kama masu hakar ma’adanai ba bisa ba tare da lasisi ba 68 a Gwagwalada a Abuja

Ya ce jami’an tsaron sun kashe mahara 25, sun kama wasu 97 sannan sun ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su.

A Kudu maso Kudu rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun kama bakin mai lita 1,442,700 da lita 154,650 na AGO.

Dakarun sun ragargaza rijiyoyin mai 18, jiragen ruwa 34, banbu biyar, manyan tanki 4, da wasu tankuna 97.

Saurar kayan da aka kama sun hada murhun dafa abinci 198, motocin 9, na’uran haƙo mai 3, jiragen ruwa 2, radio karama daya

Dakarun sun kuma kashe ‘yan bindiga 3 sun kama barayin mai 16.

A Kudu maso Gabas Buba ya ce rundunar ‘Operation UDO KA’ sun kashe mahara 21, sun kama wasu 45, sun ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su da makamai.