Home Back

YAMUTSIN SARAUTAR KANO: Ƴan sanda daga Abuja sun mamaye Gidan-Rumfa, a shirin maido da Aminu-Ado

premiumtimesng.com 2024/7/3
Don Allah Ku Saka Jihar Kano Cikin Addu’a, Suna So Su Kunna Mata Wutar Tashin Hankali, Daga Imam Murtadha Gusau

A cigaba da samun cikas da matsi da Sarki Sanusi ya ke samu a Kano tun bayan dawowarsa Sarkin Kano, A ranar Lahadi jamian ƴan sanda daka da ke zaton daga Abuja ne sun dira fadar sarki ta kodar Gidan Rumfa.

Da yake sarki Aminu Ado-Bayero mai wane s gindin murhu, tun daga Abuja ake turo jami’an tsaro su kula dashi a fadar Nasarawa, yayin da Sarki Sanusi dake Gidan Rumfa, ƴan Tauri da nafarauta ne suke gadin sa.

Bayan gwamnatin Kano ta sanar da shirin yin gyara ga fadar Nasarawa, a ranar Asabar sai ƴan sanda daga Abuja suka dira gidan Rumfa inda suka fatattaki masu gadin Sarki Sanusi.

Ga dukkan alamu dai, gwamnati daga Abuja na so su maido da sarki Aminu Ado-Bayero ne Gidan Rumfa. Sai dai kuma lamarin a cukuikuye ya ke domin hukuncin kotu ya sa an kasa samun matsaya tsakanin gwamnatin Kano, masarautar Kano da wasu daga Abuja da suke ta ya Ado-Bayero fada.

People are also reading