Home Back

Ga Duhu Ga Tsada: Yadda tsadar wutar lantarki ta jefa talakawa cikin halin ƙaƙanikayi

premiumtimesng.com 2024/5/9
Abuja Street Light
Abuja Street Light

Sanin kowa ne cewa ƴan Najeriya na kuka da tsadar sabon tsarin shan wutar lantarki a Najeriya wato tsarin rukuni-rukuni.

Bisa wannan dalili ne shirin Tambarin Talaka da Kamfanin 24 Dot ke shirya wa ta tattauna da wasu ƴan Najeriya domin jin ra’ayoyin su game da wannan sabon tsarin sha da biyan wutar lantarki a Najeriya.

Tambarin Talaka shiri ne da ya shahara wajen yin fashin baki ga muhimman lamura musamman waɗanda suka shafi talakan Najeriya.

A shirin na wannan mako jagoran shirin Abdullahi Jibrin tare da Jaafar Jega da Ahmed Umar kamar kullum sun yi muhawara ne kan batun karin kuɗin wutar lantarki da ke gasa wa talakawa aya a hannu, wanda gwamnatin Najeriya ta yi.

Jega da Umar, dukkan su sun soki wannan sabon tsari na gwamnati, inda suke cewa gwamnati ba ta yi nazari mai zurfi ba kafin ta yanke shawarar kirkiro da waɗannan sabbin tsari na wutar lantarki a kasar nan.

Jega ya ce ” Waɗanda ake basu wuta suna biya kai tsaye wato batare da siya ta hanyar mita ba, sun fi cutuwa, domin ko an baka wuta ko ba a baka wuta yawan adadin awowin da gwamnati tayi alkawari ba, idan lokacin biya ya yi za a kawo wa mutum kusan naira 100,000 kudin da zai biya. Ina aka yi wa magidanci adalci a nan.

Yan kasuwa da dama sun bayyana cewa lamarin ya jefa su cikin ƙungurmin matsi da damuwa matuka

” Muna bukatar wutar lantarki a kasuwa, amma na nawa za ka saka ya isheka har ka iya samun riba. Kuɗin wutar kawai ya isa ya cinye ribar ɗan kasuwa har ya shiga
uwar kuɗi.

People are also reading