'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Basarake Kan Auren Budurwar Shugabansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Bayanai sun fito kan kisan da ƴan bindiga suka yiwa ɗan Sarkin Hausawa na Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Safiyanu Ibrahim.
Wani ɗan uwan marigayin ya yi iƙirarin cewa an harbe shi ne saboda ya dage sai ya auri mata ta biyu wacce ta kasance budurwar shugaban ƴan bindiga.
Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2024, ƴan bindiga sun kai farmaki gidan Sarkin Hausawa na Janjala, inda suka harbe Safiyanu Ibrahim da kuma ƙaninsa, Nasiru Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɗan uwansa wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya bayyana cewa shugaban ƴan bindigan ya gargaɗi marigayin da ya ƙauracewa sabuwar amaryar tasa wacce ta fito daga jihar Zamfara.
Majiyar ta ci gaba da cewa, marigayi Safiyanu ya haɗu da matarsa ta biyu a garin Kagarko inda suka fara soyayya, amma da shugaban ƴan bindigan, wanda saurayinta ne ya samu labari, sai ya gargaɗi Safiyanu da ya janye.
"Bayan ɗaurin auren, sai amaryar ta ƙi yarda da shi, har sai da ɗaya daga cikin abokansa ya shiga cikin lamarin, amma washegari ƴan bindigan suka zo suka kashe shi."
"Amaryar ta bar gidan aurenta ne kwana guda bayan ƴan bindigan sun kashe mijinta, lamarin da ya sa danginsa suka shiga shakku domin har yanzu ba a san inda take ba.”
- Wata majiya
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna komai ba kan kisan da aka yiwa ɗan Sarkin Hausawan na Janjala har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansur Hassan ƴa ci tura domin ba a same shi ta waya ba.
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun farmaki tawagar mambobi biyar na majalisar dokokin jihar Benuwai a kan titin Makurɗi zuwa Gboko.
Shaidun ganau ba jiyau ba sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai wa ƴan majalisar hari da misalin ƙarfe 10:00 a dare a daidai kauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa Makurdi
Asali: Legit.ng