Home Back

Ko yajin aikin NLC zai dakatar da jigilar mahajjata zuwa Saudiyya?

bbc.com 2024/7/1
...

Asalin hoton, Nahcon

Yayin da Najeriya ke fama da yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadago suka fara a fadin ƙasar a yau, yajin aikin ya shafi muhimman ayyukan sassa da dama da suka haɗa da samar da wutar lantarki da ayyukan filin tashi da saukar jiragen sama waɗanda suka dogara kacokan kan wutar lantarki domin aiki.

Za a iya cewa a baya-bayan nan wannan ne yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta kira kuma ya yi tasiri matuƙa a fannonin rayuwar yau da kullum, inda yajin aikin ya zo a matsayin martani ga gazawar gwamnati wajen biyan bukatun ma’aikata.

Harwayau, yajin aikin ya kuma zo a daidai lokacin da ake jigilar alhazai zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin 2024.

Hakan dai ya sa 'yan Najeriya na dasa ayar tambaya kan ko yajin aikin zai dakatar da yadda ake ci gaba da kwashe alhazan Najeriya zuwa Saudiyyar domin gudanar da aikin hajjin na bana?

Hukumar alhazan Najeriya ta amsa tambayar

Domin samun ƙarin haske kan halin da ake ciki da kuma amsar wannan tambayar, BBC ta tuntuɓi Fatima Sanda Usara, jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar alhazai ta ƙasa, inda ta ce hukumar ba ta tunanin yajin aikin zai shafi jigilar maniyyatan.

"Muna da fahimtar cewa wannan yajin aikin ba zai shafi yadda muke kwashe alhazai zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji ba saboda shi aikin hajji abu ne da yake da ƙayyadadden lokaci."

"A yau ɗin nan ma akwai jiragen da suka tashi daga Ilorin da kuma Jigawa." In ji Fatima.

Jami'ar hulɗar ta ƙara da cewa hukumar ta san da cewa "ana iya samun ɓata garin da za su iya haifar da cikas don kansu ba wai don hukumomin filayen jirgin sama sun yarda da hakan ba."

"Amma game da wannan yajin aiki, muna nan muna magana da ma'aikatan filayen jirgin sama kuma in sha Allahu ba za a samu wannan cikas ɗin ba." Ta ƙara haske.

Da BBC ta tambaye ta hanyar da hukumar alhazan za ta bi wajen kiyaye yajin aikin kar ya shafi yadda ake kwashe alhazai zuwa Sauddiyya ganin yadda jami'an ƙungiyoyin ƙwadago ke bin ofisoshi da filayen jiragen sama suna rufe su kamar yadda suka rufe filayen jiragen sama na Legas da na Abuja, Jami'ar hulɗa da jama'ar sai ta ce.

"Ɓangaren da ake ɗiban alhazai ba ɗaya ba ne da ɓangaren da ake kwashe sauran matafiya zuwa sauran ƙasashe, ɓangaren alhazai daban ne, aikin hajji ba ɗaya ba ne da sauran tafiye-tafiye, saboda haka muna da kyakkyawar fahimtar wannan yajin aikin ba zai shafi alhazanmu ba."

'Alaƙarmu na da kyau da ƴan ƙwadago'

Fatima ta ce hukumar Alhazai na da yarjejeniya da filayen jirgin sama inda ta ƙara da cewa suna kyautata zaton cewa ƙungiyar ƙwadago suna sane da cewa aikin hajjin ba ɗaya yake da sauran tafiye-tafiye ba.

"An san da cewa musulmai ba sa ɗaukar aikin hajji da wasu da kuma muhimmancinsa a wurinsu, su kansu ƴan ƙungiyar ƙwadagon suna da wannan masaniyar."

Ta kuma ce shuwagabannin hukumar na magana da ɓangarori daban-daban yadda ya kamata saboda haka ta ce suna tunani wannan yajin aikin ba zai shafi ko dakatar da jigilar alhazai ba.

"Ko da yaushe akwai manyan da za su tsaya su kula da wannan aikin."

"Yanzu dai muna da wannan tabbaci na cewa alhazanmu in sha Allahu za su tafi ba tare da samun wani cikas ba." In ji Fatima.

Daga ƙarshe Fatima Sanda ta kuma ce hukumar alhazai ba ta da wani fargabar cewa ma'aikatan filayen jirgin sama suma za su tsunduma cikin yajin aikin.

People are also reading