Home Back

Dalilan Da Yasa Ba’a Gani Na Cikin Tawagar ‘Super Eagles’ A Halin Yanzu -Ahmed Musa

leadership.ng 2024/7/16
Dalilan Da Yasa Ba’a Gani Na Cikin Tawagar ‘Super Eagles’ A Halin Yanzu -Ahmed Musa

Kyaftin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, (Super Eagles), Ahmed Musa, ya karyata rade-radin cewa ya fice daga tawagar ‘yan wasan Nijeriya bayan shafe tsawon lokaci ba tare da ya bayyana a gaban ƴan jarida ba.

A wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida a Kaduna ranar Juma’a bayan kammala wasan sada zumunta da ya shirya wa matasan Arewacin Nijeriya, Musa ya ce batun ficewarsa daga tawagar Super Eagles ba wani abu bane face jita-jita.

Na dan tafi hutu ne kawai daga tawagar ta kasa, amma ban fice ba ina fatan zuwa gaba kaɗan zan dawo domin ci gaba da taimakawa Nijeriya wajen ganin ta lashe manyan kofuna. Cewa Musa.

Ya kuma ce yana fatan wannan bayanin nasa zai canza tunanin da dama daga cikin magoya bayansa da ke tunanin cewa ya dakata da bugawa tawagar Super Eagles kwallo.

People are also reading