Home Back

Gwamnatin Enugu ta kafa rundunar kare manoma daga makiyaya

premiumtimesng.com 2024/6/26
Fulani with cow
Fulani with cow

Gwamnatin Jihar Enugu ta bayyana cewa ta dauki ƙwaƙƙwaran matakin kare rayuka da lafiyar manoma, domin bunƙasa yalwar abinci a jihar.

Kwamishinan Harkokin Noma, Patrick Ubru, ya shaida hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Litinin, a Enugu, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta yi haɗin-gwiwa da rundunar NSCDC domin kafa Dakarun Kare Manoma, waɗanda ta kira Agro-Rangers Squard

Ubru ya ƙara da cewa kafa wannan runduna ya zama wajibi domin su taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen kare manoma da gonakin su daga makiyaya.

“An yi masu horon yadda za su kare gonakin manoma da su kan su kan su manoman da sauran kayan aikin gona na zamani domin daƙile matsalar tsaro wadda manoma ke yawan kokawa a kan ta, musamman manoman kayan gona na sayarwa da ƙananan manoman cikin jihar.

“An girke su a manyan gonaki daban-daban da kuma cibiyoyin sarrafa kayan gona.” Inji Ubru.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ma’aikatar sa na kuma tattaunawa da Ƙungiyar Miyetti Allah, domin su ma su shiga cikin rundunar, ta yadda za a samu tsaro baki ɗaya a jihar.

Ya ce: “Muna ganawa da Miyetti Allah domin su tabbatar su na hana mambobin su yi wa manoma ɓarna.

“Za su taimake mu wajen gano makiyayan da ba mambobin Miyetti Allah ba ne, waɗanda ke kutsawa cikin Jihar Enugu suna haifar da rashin fahimta tsakanin makiyaya da manoma.”

Da ya ke magana kan rikicin da aka yi tsakanin manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Isi-Uzo, Kwamishina Ubru ya ce Gwamnatin Jiha ta haɗa kai da Gwamnatin Tarayya an girke sansanin sojoji a Isi-Uzo.

“Nan ba daɗewa ba rikicin manoma da makiyaya da karakainar da wasu masu yawo da makamai a hannu ke yi, duk za su zama tarihi.” Inji shi.

People are also reading