Home Back

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya a Arewa

legit.ng 2024/7/1
  • Wasu maharan sun tare daliban jami'a mata, sun yi awon gaɓa da su a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai ranar Asabar
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa an sace ɗalibai mata biyu na jami'ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM)
  • Ta ce tuni jami'an ƴan sanda suka fara bincike domin kubutar da ɗaliban bayan samun rahoto daga hukumar jami'ar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Laraba ta tabbatar da sace wasu dalibai mata biyu na jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM).

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an yi garkuwa da daliban biyu ne a daren ranar Asabar a kan hanyar zuwa jami’ar wacce a baya ake kiranta da sunan jami'ar noma ta tarayya (FUAM).

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
An yi garkuwa da ɗaliban jami'a mata a jihar Benuwai Hoto: Nigeria Police Force Asali: Twitter

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sanda reshen jihar, SP Catherine Anene ce ta tabbatar da sace ɗaliban ga manema labarai a Makurɗi, babban birnin Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan ba ta ambaci sunayen ɗaliban da aka yi garkuwa da su ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amma Anene ta yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar ta gabata da misalin karfe 11 na dare a kan titin North Bank/UniAgric dake Makurdi.

Ta kuma tabbatar da cewa harin da aka kai har aka ɗauke ɗaliban ya faru ne. a wajen makaranta amma ba a cikin harabar jami'a ba.

Ta ce masu garkuwar da mutanen sun tare hanya, kana suka ɗauki ɗaliban da lamarin da shafa, suka tafi da su kafin jami’an tsaro su isa wurin.

Anene ta ce runi iyalan ɗaliban da aka sace da hukumar makarantar suka sanar da ‘yan sanda kuma tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin, cewar Daily Post.

Mataimakiyar rijistara mai kula da sashin yada labarai da hulda da jama'a, Misis Lucy Iwodi, ta shaida wa manema labarai lokacin da aka tuntube ta cewa ba ta samu izinin yin magana kan lamarin ba.

Ƴan bindiga sun farmaki kasuwa a Kaduna

A wani labarin ƴan ta'adda ɗauke da makamai sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru da tsakar rana a ranar Laraba, 29 gs watan Mayun 2024.

Maharan sun kai harin ne a kasuwar Kwanar Maro a gundumar Maro a ƙaramar hukumar yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

People are also reading