Kano: “Zaman ’Yan Tauri a Fadar Sarki Sanusi II Ya Jefa Fargaba a Zukatan Jama’a” Dambazau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Mazauna jihar Kano, musamman makwaftan fadar Sarkin Kano, sun koka kan yawaitar 'yan tauri a yankin fadar.
Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa 'yan tauri sun yi wa fadar Sarkin Kano tsinke domin ba da tsaro ga Muhammadu Sanusi II.
Daboon Dambazau, wani ma'abocin shafin X ya bayyana cewa ayyukan 'yan tauri a yankin ya jefa tsoro a zukatan jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dambazau ya ce:
"A cikin kwana bakwai da suka gabata, an samu karuwar adadin 'yan tauri a yankin fadar Sarkin Kano.
"Ayyukan da suke yi ya jefa tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin, wanda ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum."
Daboon Dambazau ya yi kira ga jami'an tsaro da su dauki matakin gaggawa a kan lamarin, yayin da wallafa bidiyon 'yan taurin.
Kalli faifan bidiyo daban daban a kasa:
Shi ma wani ma'abocin shafin na X, Kawu Garba wanda ya wallafa bidoyon 'yan tauri da suka taru a fadar Sarkin Kano ya koka kan cewa:
"Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kasance mai da'awar yaki da cusa yaran talakawa a harkar dabanci.
"Sai dai kuma yanzu sarkin ya kasa cewa uffan kan abin da ke faruwa a fada. Wannan abin takaici ne da yaudara, la'akari da matsayarsa a baya."
@Olowolagba39300 ya ce:
"Idan 'yan siyasa sun bar kan mulki, suna fadin gaskiya, amma da sun samu mulki sai su shafawa idanunsu toka."
@Princedansadauk ya ce:
"Dama dai 'yayan talakawa ne ke zarginsa a kan hakan, amma ka ga yanzu sai ya kyale su su yi abin da suka fi so. Ina da tabbacin ba shi ya gayyace ba."
A wani labarin, mun ruwaito cewa hudubar Sallar Juma'a da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gabatar ta jawo cece-kuce kuce.
A yayin da sarkin ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya ja da hukuncin Allah, Muaz Magaji, ya soki Sanusi II da cewa ya yi hubar ne domin yin habaici.
Asali: Legit.ng