Home Back

NAHCON Ta Faɗi Dalilin Rashin Fara Jigilar Alhazan Kano da Wasu Jihohi 6, Ta Gama da Nasarawa

legit.ng 2024/9/27
  • Yau Laraba za a fara jigilar alhazan jihohin Kano, Kaduna da wasu jihohin Arewa zuwa ƙasa mai tsarki bayan kammala kwashe maniyyatar Nasarawa
  • Hukumar NAHCON ce ta bayyana haka a wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, mai magana da yawun hukumar ta rattaɓawa hannu
  • Ta shawarci maniyyata su kwaɓtar da hankalinsu domin duk wanda ya fara tafiya shi zai fara dawowa gida bayan kammala aikin hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da cewa ta kammala jigilar maniyyatan jihar Nasarawa zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fadima Sanda Usara ta fitar fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.

Jigilar alhazai.
Za a fara kwashe alhazan Kano, Kaduna da wasu jihohi zuwa Saudiyya yau Laraba Hoto: NAHCON Asali: Facebook

Ta ce maniyyatan jihohin Kaduna, Kano, Borno, Yobe da Adamawa za su fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki yau Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin farin ciki, jihar Nasarawa ce ta farko da ta kammala jigilar maniyyatan ta guda 1,794 zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana 2024.

"Jiya Talata da daddare ake tsamnanin jihar Oyo da hukumomin tsaro za su kammala kwashe maniyyatan su, sawu ɗaya ya rage ma kowanen su."

- Fatima.Usara.

Za a fara kwashe alhazan Kano da Kaduna

Mai magana da yawun NAHCON ta ƙara da cewa a halin yanzun za a shiga mako na biyu bayan fara jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudi Arabia.

Ta ce jihohin da za su fara jigilar alhazan su yau Laraba sun hada da jihohin Kaduna, Yobe, Kano, Adamawa, Borno, da Sokoto da Filato.

Hukumar ta kuma buƙaci maniyyatan da su kwantar da hankalinsu kan rashin kwashe su domin NAHCON tana da tsarin na farko tafiya shi ne na farko a dawowa.

Fatima ta ce kowane maniyyaci zai kwashe kwanaki daidai da kowa a ƙasa mai tsarki, babu wanda zai fi wani.

Ta kuma ƙara da cewa MAHCON ta samu nasarar jigilar alhazai sama da 10,000 kawo yanzu kuma babu jirgin da aka soke bayan kammala shirin tashinsa.

Naira ta kara farfaɗowa

A wani rahoton kuma Ƙimar Naira ta ƙara sama a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata sa'o'i 24 bayan kuɗin Najeriya sun rikita Dalar Amurka.

Rahoton FMDQ na ranar Talata ya nuna cewa Naira ta tashi da N3.31 inda aka yi musayar kowace Dalar Amurka kan N1,465.68.

Asali: Legit.ng

People are also reading