Home Back

‘Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Rarara

leadership.ng 4 days ago
‘Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Rarara

A daren jiya Alhamis da misalin Karfe 1 na wayewar garin Juma’a, wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun shiga Garin Kahutu da ke yankin Ƙaramar hukumar Ɗanja a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Hajiya Halima Adamu, mahaifiya ga shahararren mawakin nan Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Rahotannin da muka samu daga ƙauyen sun nuna cewa, maharan sun shiga kauyen ne a ƙafa a sirrince ba tare da yin harbi ba a lokacin da suke gudanar da ta’annacin nasu.

Sun dauki ‘yan mintuna suna farmaki kuma gyatumar ba ta yi musu gardama ba lokacin da suka bukaci ta bi su kamar yadda muka samu labari.

An bayyana cewa akwai sauran mutane a cikin gidan, amma maharan suka zabi ɗaukar mahaifiyar Rarara, inda suka bar sauran kuma ba wanda ya yi ƙoƙarin martani ga maharan.

Ana zaton maharan sun ajiye ababen hawansu a wani wuri inda suka taka da ƙafa wajen shiga ƙauyen.

Jin ta bakin shahararren mawaƙin ya ci tura kasancewar baya ɗaga wayarsa a idan an kira.

People are also reading