Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/17
Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya 

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa, ta amince da karin kudin wutar lantarki da ‘yan Nijeriya ke biya.

Mataimakin shugaban hukumar, Musliu Oseni ya shaida wa taron manema labarai a Abuja, inda ya ce kwastomomi za su rika biyan Naira 225 na kilowat cikin sa’a guda, sabanin Naira 66 da suka saba biya a baya.

Kwastamomin da ke karkashin rukunin A, na shan wutar lantarki na tsawon sa’o’i 20 a kullum.

Oseni ya ce, wadannan kwastamomin na wakiltar kashi 15 na mutanen da ke biyan kudi don shan wutar lantarkin a Nijeriya.

Ya kara da cewa, sun kuma mayar da wasu kwastamominsu zuwa rukunin B daga rukunin A na masu shan wutar lantarkin saboda rashin ba su wutar na tsawon sa’o’i 20 a kowace rana.

Sai dai jami’n ya ce, sabon tsarin karin kudin ba zai shafi sauran kwastomomin da ke shan wutar lantarki a karkashin sauran rukunin ba.

Tashin Farashin Gas Ne Ya Kawo Karin Kudin Lantarki 

Da ma matakin hukumar da ke kula da hada-hadar albarkatun man fetur na karin farashin gas ya sanya fargabar yiwuwar farashin lantarki ya karu a sassan Nijeriya, daidai lokacin da hukumar lantarkin ke sanar da karuwar mutanen da ke amfani da mita.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Farouk Ahmed ta bukaci kara farashin gas din da ake sayarwa kamfanonin rarraba lantarki daga farashin dala bitu da centi 18 kan kowanne cubic zuwa dala biyu da centi 42.

Kazalika, sanarwar ta nemi kara farashin gas din da ake sayarwa daidaikun jama’a zuwa dala biyu da centi 92 daga dala biyu da centi 50 da ake sayarwa a baya.

A cewar Farouk, matakin da hukumar ta dauka ya yi daidai da tanadin sashe na 167 na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021 da ta sahale bibiyar farashin da kuma sauya shi lokaci zuwa lokaci.

People are also reading