Home Back

‘Yan Arewa sun zama ‘yan-amshin-Shata Gwamnatin Tinubu – Lukman, tsohon Mataimakin Shugaban APC

premiumtimesng.com 4 days ago
‘Yan Arewa sun zama ‘yan-amshin-Shata Gwamnatin Tinubu – Lukman, tsohon Mataimakin Shugaban APC

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya ragargaji ‘yan siyasar Arewa da ke cikin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, cewa an sun yi sototo, su na kallo an maida su ‘yan-amshin-Shata.

Lukman wanda kwanan nan ya fice daga APC, ya ce, “an maida ‘yan siyasar Arewa “an-amshin-Shata a gwamnatin Tinubu, waɗanda hatta shi kan sa amshin ba su iya ba. Ga shi kuma su na sane da cewa wanda suke wa amshi shi ma bai san makamar aikin sa ba.”

Ya ce ‘yan Arewa sun samu cikakkiyar damar farfaɗo da yankin su tare da saisaita shi a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, amma abin takaici ba su yi amfani da damar ba.

Lukman ya yi wannan bayani cikin wata zazzafar buɗaɗɗiyar wasiƙar da ya yi wa ‘yan siyasar Arewa.

A cikin wasiƙar wadda ya rubuta da Turanci, kuma mai tsawon gaske, ‘Explosive North: Open Letter to Northern Politicians’, wato ‘Ƙaryar Arewa Ta Ƙare: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga ‘Yan Siyasar Arewa’, Lukman ya ce ‘yan siyasar Arewa su yi hattara, saboda irin raɗaɗin yunwar da ke rarakar ‘yan Arewa a kowane yanki, za ta iya sa a fara afkawa cikin gidajen mutane ana kwasar abinci da dukiyoyin.

Wasiƙar wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES HAUSA, ta yi nuni da cewa: “Yanzu dai shekara ɗaya ya wuce a mulkin Shugaba Bola Tinubu. Su kuma ‘yan siyasar Arewa sai lagon su ke ƙara karyewa, su na ƙara wargajewa, babu tsari. Shi kan sa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya kamata a ce shi ne ya zama bangon jingina ko jagaban Arewa, amma ya zama ‘magen Lami, ba cizo ba yakushi.”

“Da wuya ka samu wani jigo ɗan Arewa a cikin gwamnatin Tinubu, har Shettima ɗin, wanda zai iya tashi tsaye ya kare martaba da muradin Arewa.

“Abin takaici duk sun maida hankula wajen gina kan su ba gina Arewa ba.

Lukman ya kuma ce hatta Ofishin Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, duk sun zama ‘yan-amshin-Shata.

People are also reading