Home Back

Zamu bai wa fannin masana’anatar Fatu da Ƙiraga mahimmanci domin samawa matasa aikin yi – Gwamnatin tarayya

dalafmkano.com 2024/7/1

Gwamnatin tarayya ta ce a ƙoƙarin ta na farfaɗo da harkokin sana’ar Fatu da Ƙiraga a ƙasar nan, ta ce za ta ƙara bai wa fannin mahimmanci, domin samawa al’umma musamman ma matasa aikin yi da za su dogara da kan su, tare da rage musu rashin aikin yi a ƙasa.

Ministan ma’aikatar Ƙirƙira da Fasaha ta ƙasa Cheif Uche G Nnaji, ne ya bayyana hakan, a yayin taron ƙaddamar da cibiyar sarrafa Fatu da Ƙiraga, da kwalejin koyon ayyukan sarrafa Fatu ta NILEST, ta gina a ofishin shiryar da ke garin Zawaciki a nan Kano, wanda taron ya gudana a ƙarshen makon nan.

Ministan da ya samu wakilcin Darakta Chemical na ma’aikatar ƙirƙira da Fasaha ta ƙasa Dakta Bassey, ya ce, samar da sashin koyar da sanin fatu da ƙiraga da cibiyar ta NILEST, tayi a nan Kano, abu ne da zai taimakawa matasa wajen samun aikin yi, ta yadda za su dogara da kan su, tare kuma da rage musu rashin aikin yi a faɗin ƙasa.

Da yake nasa jawabin daraktan cibiyar sarrafa Fatu da Ƙiraga ta NILEST, a ƙasar nan, Farfesa Muhammed Kabir Yakubu, ya shaidawa Dala FM Kano, cewa, yawan cin naman Ganda da da mutane ke yi na Fatar Dabbobi, da ƙarancin wutar lantarki a ƙasa, na daga cikin babban kalubalen a harkar sarrafa Fatu da Ƙiraga.

Farfesa Muhammed Kabir Yakubu, ya kuma yi kira ga matasa da su ƙara tashi tsaye wajen riƙo da ƙananan sana’o’i ta yadda za su rinƙa dogaro da kan su a faɗin ƙasar nan.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mafi yawan matasa ke fuskantar ƙarancin abun yi a sassan ƙasar nan, lamarin da hakan kan haifar musu da koma baya a rayuwar su, fatan dai kowanne ɓangare za’ayi abinda ya dace, dan ganin al’umma musamman ma Matasan sun fice daga cikin halin rashin aikin yin a ƙasa.

People are also reading