Home Back

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu sun kwato makamai da dama a Benuwai

premiumtimesng.com 2024/5/15
TSUMAGIYAR KAN HANYA: An umarci ‘yan sandan Abuja su riƙa binciken motar ko wa kuma ko ɗan wa

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ‘yan bindiga biyu sannan sun kama makamai a karamar hukumar Katsina-Ala.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sewuese Anene ya sanar da haka ranar Laraba a garin Makurdi.

Anene ya ce ‘yan sandan sun samu nasarar kashe wadannan mahara bayan sun samu labarin cewa maharan sun yi dandazo a kauyen De-Mtsa dake karamar hukumar Katsina-Ala suna shirin kai wa mutane hari.

Ya ce bayan haka ne a ranar 27 ga Maris dakarun rundunar ‘Operation Zenda Joint Task Force (JTF)’ a karkashin jagorancin kwamandan rundunar Felix Nomiyugh suka kai wa maharan hari a kauyen.

“Jami’an tsaron sun kashe mutum biyu, sun kama mutum daya sannan sauran sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.

“Jami’an tsaron za su ci gaba da farautar maharan domin kamo su da ganin an yanke musu hukunci.

“Dakarun sun kwato bindiga kirar 06 Rifle, harsasan AK-47, wasu harsasai 80, rigunan sojoji da wayoyin hannu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Emmanuel Adesina ya yaba kokarin da jami’an tsaron ke yi inda ya hore su da su ci gaba fatattakar yan bindiga aduk inda suke a fadin jihar.

Adesina ya yi kira ga mutane da su ci gaba da ba jami’an tsaro baya domin samun nasara a yankin da suke yi da ta’addanci a jihar.

People are also reading