Home Back

“Dalilin da Yasa Muka Saki Mutane 313 da Muka Kama Bisa Zargin Ta’addanci a Borno,” Sojoji

legit.ng 2024/5/10
  • Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta saki mutane 313 da ta kama a jihar Borno bisa zargin ta'addanci, ta mika su ga gwamnatin jihar
  • Kakakin hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an saki mutanen ne bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke Maiduguri
  • Haka zalika, Buba ya ce dakarun soji da ke aiki a Borno da Gombe sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a wannan mako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Hedikwatar tsaro ta ce ta mika mutane 313 da ta kama ga gwamnatin Borno bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri.

Rundunar soji ta yi magana kan sakin mutane 313 da ta kama a Borno
Hedikwatar tsaro ta ce ta mika mutanen ga gwamnatin jihar Borno. Hoyo: @HQNigerianArmy Asali: Twitter

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Ba a kama su da laifin ta'addanci ba?

Buba ya ce ana tsare da wadanda aka kaman ne bisa tuhuma, amma ba a samu wata shaida a kansu ba a lokacin da aka kammala bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ma’aikatar shari’a ta tarayya ce ta gabatar da kararrakin, inda kotun ta bayar da umarnin a sake su.

"A bisa ga haka an mika su ga gwamnatin jihar Borno domin daukar mataki na gaba"

- Inji kakin rundunar sojoji

A halin da ake ciki kuma dakarun Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP.

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

A wani rahoton na jaridar Vanguard, sojojin sun kashe 'yan ta'adda da dama tare da kame abokan aikinsu a cikin wannan mako.

Buba ya ce wasu kwamandojin ‘yan ta’adda da mayaka sun mika wuya ga sojojin da ke gudanar da aiki a kananan hukumomin jihar Borno da Adamawa.

A cewarsa, rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ta kai wasu hare-hare ta sama kan ‘yan ta’adda a Arina Woje da Tumbum Shitu kusa da tafkin Chadi a ranakun 22 da 24 ga watan Maris.

'Yan ta'adda sun kashe jami'an tsaron Borno

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa mayakan Boko Haram sun yi wa wasu sojoji da jami'an tsaro kwantan ɓauna a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin arangamar, an kashe soja daya da jami'an tsaro biyu.

Asali: Legit.ng

People are also reading