Home Back

Burina Na Yi Rubutun Da Ko Ba Ni A Yi Alfahari Da Shi Ba Na Allah Wadai Ba – Mustapha

leadership.ng 2024/5/16
Burina Na Yi Rubutun Da Ko Ba Ni A Yi Alfahari Da Shi Ba Na Allah Wadai Ba – Mustapha

Daya daga cikin marubuta littattafan Hausa na yanar gizo MUSTAPHA ABDULLAHI ABUBAKAR, ya bayyanawa masu karatu babban dalilin da ya sa ya tsunduma harkar rubutu tare da abin da ya ke son cimma game da rubutu, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarsa. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:

Da farko za ka fara fada wa masu karatu cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka…

Sunana Mustapha Abdullahi Abubakar, an haifi ni a Rimin Zayam da ke  karamar Hukumar toro na jihar Bauchi. Na yi karatun ‘Nursary and Primary’ a ‘L.E.A Primary School’ da ke karamar hukumar Jos ta kudu na Jihar filato wato Jos. Inda cikin yarda Allah na ci gaba da karatuna na sakandare a ‘Nurul Islam High School’ duk a garin Jos Jihar filato. Inda yanzu na samu shadar kammala karatuna na aikin jarida a kwalejin kimiya da fasaha na  ‘Abubakar Tatari Ali Polytechnic’, da ke jihar Bauchi. Inda yanzu haka na ci gaba da karatuna na HND duka a garin Bauchi.

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar rubutu?

Abin da ya ja hankali na fara Rubutu shi ne yaudarar da a ka yi min lokacin ina soyayya da wata wacce ta yaudare ni shi ne dalilina na fara rubutu.

Rubutun

Kamar wane labari ka fi maida hankali a kai wajen rubutawa?

Labarin da na fi maida hankali shi ne labaran hikayoyi, da kuma na soyayya.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

Gaskiya ne na yi gwagwarmaya sosai, duba da lokacin ban ma san ta ya ya zan fara yin rubutun ba, da kuma salon rubutun da zan yi.

Za ka yi kamar shekara nawa da fara rubutu?

Na kai shekaru biyar ina rubutu.

Ka rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?

Gaskiya na yi rubutun labari da yawa  kamar; Akwai Dalili, Tarbiya A yau, Mai Hakuri, Rayuwar Addini, Dan Baiwa, Bakar Alaka.

Wane labari ne ya zamo bakandamiyarka cikin labaran da ka rubuta?

A cikin rubutuna da na yi bakandamiyata shi ne ‘Akwai Dalili” wanda na fi so kenan, kusan dukka labarin soyayyata ne.

Wane labari ne cikin labaranka ya fi ba ka wahala wajen rubutawa, kuma me ya sa?

Wanda ya fi ba ni wahala shi ne ‘A kwai Dalili’, domin lokacin da nake rubutun littafin yana tuna min abubuwa da dama game da rayuwata, da wacce muka yi soyayya.

Wane irin nasarori ka samu game da rubutu?

Nasarorin da na samu shi ne na Hadu da manyan marubuta wanda nake kallo a TB ko jin labaransu a gidajan rediyo, kamar Alan waka, Abba Abubakar Yakubu daga Jos, Fadila H. Aliyu, da sauran marubuta da dama, sai dai na ce Ma sha Allah.

Wanne irin kalubale ka fuskanta game da rubutu?

Kamar yadda na ce na samu kalubale sosai, kama daga ‘yan’uwana da ma abokai na, amma yanzu dai Alhamdullahi.

Lokacin da ka fara sanar wa iyayenka kana son fara yin rubutu, ko a kwai wani kalubale da ka fuskanta daga gare su?

Gaskiya ban fuskanci wani kalubale daga iyayena ba, sai dai ma  fatan nasara daga bakinsu.

A gabadaya labaran da ka rubuta shin ka taba buga wani?

Ban buga littafi ko daya ba yanzu haka, amma a kwai wanda yanzu haka saura kadan ya fito kasuwa da yardar Allah.

Mene ne burinka na gaba game da rubutu?

Burina a harkar rubutu shi ne na yi rubutu wanda ko ba ni a raye a yi alfahari da shi ba wanda za a rika Allah wadai da shi ba.

Wane abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka game da rubutu?

Na samu yabo daga wajan mutane da dama gaskiya, an taba batamin rai sau daya dalili kuwa shi ne labarin soyayyata dana rubuta.

Me ka fi yawan tunawa game da rubutu?

Na fi tunawa da cewa komai zan rubuta iyayena za su karanta, abin da nake tunawa kenan.

Ya ka dauki rubutu a wajenka?

Na dauki rubutun sana’a ce kamar ko wacce sana’a.

Bayan rubutu kana wata sana’ar ne?

Bayan rubutu, ni ma’akacin gidan Rediyo ne a garin Jos.

Ya ka ke iya hada rubutunka da aikinka?

A kwai lokacin da nake warewa na yin rubutu da kuma lokacin sana’a ta.

Kamar yaushe ka fi jin dadin yin rubutu?

Na fi yin rubutu cikin dare gaskiya, Kamar karfe 10 na dare zuwa’ 12 na dare.

Me za ka ce da makaranta labaranka?

Ina godiya sosai da irin shawarware da suke ba ni da kuma fatan Alkhari da suke yi min, Allah ubangeji ya bar zumunci.

Ko kanada wadanda za ka gaisar?

Ina gaishe da mahaifina da mahaifiyata da kuma Abba Abubakar Yakubu Dan Jarida sosai a garin Jos da duk masoya Manzon Allah (SAW).

People are also reading