Gwamna Ya Waiwayi Ma'aikata, Ya Bayar da Umarnin a Tura Masu Kuɗi Kafin Babbar Sallah
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da umarnin a biya ma'aikata albashin watan Yuni gabanin ranar Babbar Sallah.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren ofishin shugaban ma'aikatan jihar Yobe Alhaji Bukar Kilo, ya fitar a madadin shugaban ma'aikatan jihar.
Ya ce Mai Girma Gwamna Buni ya umarci ma'aikatar kudi da ma'aikatar ƙananan hukumomi su tabbatar sun turawa ma'aikata albashin watan Yunin kafin Sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin taimakawa ma'aikata su yi shagalin Sallah cikin walwala da jin daɗi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
"Wannan matakin na taimakawa ma'aikata da tallafin kuɗi ya nuna yadda mai girma gwamna ke tausayin ma'aikatan gwamnati a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa.
"A cikin ƙanƙani. lokaci gwamna ya ba ma'aikatan jiha da na kananan hukumomi tallafin kuɗi domin rage raɗaɗin wahalar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan," in ji sanarwan.
Idan baku manta ba Gwamna Buni ya bayar da kyautar N15,000 da N10,000 ga ma'aikatan jiha, ƙananan hukumomi da ƴan fansho domin rage raɗaɗi.
Daga ƙarshe sanarwar ta miƙa sakon taya murna ga ɗaukacin ma'aikatan gwamna yayin da suke shirin babbar Sallah, jaridar Punch ta ruwaito.
Idan Allah ya kaimu ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2024 Musulmi za su gudanar da idin Babbar Sallah kamar yadda fadar Sarkin Musulmi ta sanar.
A wani rahoton kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje na ci gaba da fuskantar matsin lamba yayin da aka sake maka shi a gaban kotu.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ce za ta fara sauraron gundarin karar da aka nemi sauke Ganduje daga shugabancin APC.
Asali: Legit.ng