Home Back

Gwamna Ya Waiwayi Ma'aikata, Ya Bayar da Umarnin a Tura Masu Kuɗi Kafin Babbar Sallah

legit.ng 2024/7/5
  • Yayin da ake shirin babbar Sallah, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci a biya ma'aikatan gwamnati albashin watan Yuni a jihar Yobe
  • Babban sakataren hukumar kula da ma'aikata na jihar, Alhaji Bukar Kilo ne ya bayyana haka a madadin shugaban ma'aikatan
  • Ya ce wannan mataki na kara nuna yadda mai girma gwamna ke son kulawa da walwala da jin daɗin ma'aikatan jihar Yobe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da umarnin a biya ma'aikata albashin watan Yuni gabanin ranar Babbar Sallah.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren ofishin shugaban ma'aikatan jihar Yobe Alhaji Bukar Kilo, ya fitar a madadin shugaban ma'aikatan jihar.

Gwamna Mai Mala Buni.
Gwamnan Yobe ya amince a biya ma'aikata albashin watan Yuni Hoto: Hon Mai Mala Buni Asali: Twitter

Ya ce Mai Girma Gwamna Buni ya umarci ma'aikatar kudi da ma'aikatar ƙananan hukumomi su tabbatar sun turawa ma'aikata albashin watan Yunin kafin Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin taimakawa ma'aikata su yi shagalin Sallah cikin walwala da jin daɗi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

"Wannan matakin na taimakawa ma'aikata da tallafin kuɗi ya nuna yadda mai girma gwamna ke tausayin ma'aikatan gwamnati a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa.
"A cikin ƙanƙani. lokaci gwamna ya ba ma'aikatan jiha da na kananan hukumomi tallafin kuɗi domin rage raɗaɗin wahalar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan," in ji sanarwan.

Idan baku manta ba Gwamna Buni ya bayar da kyautar N15,000 da N10,000 ga ma'aikatan jiha, ƙananan hukumomi da ƴan fansho domin rage raɗaɗi.

Daga ƙarshe sanarwar ta miƙa sakon taya murna ga ɗaukacin ma'aikatan gwamna yayin da suke shirin babbar Sallah, jaridar Punch ta ruwaito.

Idan Allah ya kaimu ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2024 Musulmi za su gudanar da idin Babbar Sallah kamar yadda fadar Sarkin Musulmi ta sanar.

An ƙara taso Ganduje a APC

A wani rahoton kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje na ci gaba da fuskantar matsin lamba yayin da aka sake maka shi a gaban kotu.

Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ce za ta fara sauraron gundarin karar da aka nemi sauke Ganduje daga shugabancin APC.

Asali: Legit.ng

People are also reading