Home Back

Ukraine: NATO na samun turjiyar Hangari

dw.com 2024/7/3
 Jens Stoltenberg | NATO | Ukraine | Tallafi
Sakatare janar na kungiyar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg

Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyar Kawancen Tsaron ta NATO ke dari-dari da kasar Hangari da ke mammaba a kungiyar kuma zama kawa daya tilo ga Rasha. Hangarin ta jima da nuna kin amincewarta da bai wa Ukraine tallafin makamai da sunan kungiyar, wanda a cewar mahukuntan Budapest hakan ka iya kai NATO da Rasha ga yaki. A yanzu haka ma, kungiyar na fuskantar turjiya daga firaminista Victor Orban. Sai dai bayan wata ziyara da sakatare janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya kai masa, sun cimma yarjejeniya a kan cewa kasar Hangari ba za ta hana ba kuma ba za a yi da ita ba. Wannan dai shi ne karon farko da kasashe mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, ke shirin aika makamai zuwa Ukraine da sunan kungiyar da ta jima tana kallon Rasha a matasayin wata barazana ga Turai.

Kungiyar NATO dai ta sha alwashin sama da tallafin kimanin dalar Amurka biliyan 40 ga Ukraine a kowace shekara, har sai sanda yakinta da Rasha ya kawo karshe. To sai dai, tana kokarin yin kaffa-kaffa domin gudun fadawa yaki kai tsaye da Rashan. Masharhanta na ganin matakin da Hangari ta dauka ka iya zama cikas ga kungiyar ta NATO, kasancewar Firaminsta Orban ya jima yana kokarin samar da sulhu a tsakanin kungiyar da Rasha na cewar ba lallai ba ne a koda yaushe ra'ayi ya zamanto daya. A watan Yulin gobe ne kungiyar ta NATO za ta gudanar da babban taronta a kan sabbin hanyoyin da zasu fito da su na ci gaba da bai wa Ukraine tallafi, a daidai lokacin da take fargabar yiwuwar dawowar tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan madafun iko. Amurkan dai na zaman wadda ta fi bayar da kaso mai tsoka ta  fuskacin gudanar da kungiyar ta NATO, kuma ana hasashen dawowar Trump ka iya kawo cikas.

People are also reading