Home Back

Kantoman Goronyo Tare Hadin Gwiwar Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Mafakar “Yan Ta’adda

daybreak.ng 2024/10/6

A Kokarin Kantoman mulki na Goronyo Alh Kabiru S/ Fulani da dan Majalisar Jaha Mai Wakiltar Goronyo Nasiru Adamu na kawar da ta’addanci a Karamar Hukumar Mulki ta Goronyo.

Sun Jagoranci Jami’an Tsaro domin tarwatsa mafakar Yan Ta’adda a dazukan Giyawa ta Karamar Hukumar Mulkin Goronyo.

Tawagar Jami’an Tsaro wadda Kantoman Goronyo da Dan Majalisar Jaha Mai Wakiltar Goronyo suka Jagoranta sunkai samame a maboyar Yan Bindiga dake cikin dajin Giyawa.

Wannan yunkuri na cikin jajircewar Kantoman Goronyo da dan Majalisar Jaha mai wakiltar Goronyo a bisa jajircewar su tareda baiwa Jami’an Tsaro cikakkiyar kulawa akan aikin su.

Sun jagoranci Jami’an Tsaro da Al’ummar gari an kutsa a dajin Giyawa inda aka samu nasarar tarwatsa mafakar Yan Ta’adda.

People are also reading