Malamin Addini Ya Rasa Ransa Bayan Ɗansa Ya Yi Ajalinsa Yana Bacci, an Gano Dalili
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - An shiga wani irin yanayi bayan ɗa ya kashe mahaifinsa yana tsaka da bacci.
Marigayin Isaac Umurie wanda babban Fasto ne ya rasa ransa bayan ɗansa ya yi ajalinsa yana bacci a jihar Delta.
Lamarin ya faru ne da daren yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024 a Okpare da ke karamar hukumar Ughelli ya Kudu, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanda ake zargin mai suna Ufuoma Umurie ya kuma kai hari kan mahaifiyarsa da ta yi kokarin kare mijinta.
An ruwaito cewa da kyar mahaifiyarsa ta sha inda ta tsira da saran adda daga ɗan nata da tsakar dare.
Wasu majiyoyi sun tabbatar cewa wannan shi ne karo na biyu da ɗan ke farautar ran mahaifinsa a yankin.
Jama'a sun yi kokarin kawo dauki amma kafin zuwan su ma ɗan ya riga ya aikata laifin na kisan mahaifin nasa.
Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Umurie yana hannunsu.
Edafe ya tabbatar da cewa ana zargin matashin yana fama da ciwon ƙwaƙwalwa inda aka fara bincike.
Ya tabbatar da cewa za a hukunta shi dai-dai da laifinsa da zaran an kammala bincike kan lamarin.
A wani labarin, kun ji cewa ƴan sanda a jihar Delta sun sanar da kama ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne da wasu matsafa dauke da gashin mutum.
Dan bindigar da aka fara kamawa mai suna Favour Eze, dan shekaru 24 ya fito ne daga ƙaramar hukumar Afikpo da ke jihar Ebonyi.
Asali: Legit.ng