Home Back

Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Hukumar EFCC Ya Salwantar da Ransa

legit.ng 2024/10/5
  • Wani jami'in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ya yanke wata gurguwar shawara mara daɗin ji a birnin tarayya Abuja
  • Jami'in wanda ba a bayyana sunansa ba ya kashe kansa a cikin gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yulin 2024
  • Kakakin hukumar EFCC wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jami’in hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.

Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Jami'in EFCC ya mutu a Abuja
Jami'in EFCC ya kashe kansa a Abuja Hoto: @OfficialEFCC Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce marigayin wanda ba a bayyana sunansa ba ya kasance mamba na kwas 5 a kwalejin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumar EFCC ta ce kan lamarin?

Da yake magana kan lamarin, kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa hukumar na binciko wasu abubuwan da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da ƙalubalen iyali da ka iya sanyawa jami'in ya yanke shawarar barin duniya.

Dele Oyewale ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko bayyana sunan jami’in ba har sai an kammala binciken da ake gudanarwa.

Sai dai, wasu majiyoyi daga hukumar sun shaidawa jaridar PM News cewa jami’in ya daɗe yana samun samun matsala da wata mace wacce shugabarsa ce a wajen aiki.

An umarci a cafke jami'an hukumar EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC ya ba da umarnin a kama wasu jami'an hukumar guda biyu da suka kai samame ɗakunan wani otel a jihar Legas.

Mista Ola Olukoyede ya ba da umarnin cafke jami'an ne bayan an gansu a bidiyo suna cin zarafin wata ma'aikaciyar otel din da suka kai samamen.

Asali: Legit.ng

People are also reading