Home Back

Wutar lantarki za ta wadata a ko’ina a fadin Kasar nan, nan da watanni 6 masu zuwa – Minista

premiumtimesng.com 2024/4/29
Ministan Makamashi ya bayyana dalilan ƙara taɓarɓarewar wutar lantarki a Najeriya

Ministan makamashi Adebayo Adelabu ya ce nan da watanni uku zuwa shida masu zuwa za a warware matsalolin da suka dabaibaye samar da wutar lantarki a kasar nan.

Adelabu ya fadi haka ne a makon jiya yayin da ya kai ziyar duba na’urorin samar da wutar lantarki dake Maryland da Alausa a jihar Legas.

Ya ce zuwa yanzu aikin inganta wasu tashoshin a Legas da Kamfanin raba wutar lantarki ta kasa ke yi ya yi nisa kuma ana yin su yadda ya kamata.

Adeelabu ya kara da cewa raba wutar lantarki da kamfanonin DisCos ke yi ya ragu ne saboda rashin kudaden da kamfanonin ke bukata domin inganta aiyukansu.

Adelabu ya ce gwamnati za ta yi kokari wajen ganin kamfanonin DisCos sun inganta aiyukan babu kakkautawa.

Adelabu ya tabbatar cewa ma’aikatar za ta yi kokarin wajen ganin ta inganta aiyukanta domin moriyar kowa da kowa a kasarnan.

 
People are also reading