Home Back

Tsaraba Ga Amaren Bayan Sallah Da Masu Niyyar Aure

leadership.ng 2024/5/1
Tsaraba Ga Amaren Bayan Sallah Da Masu Niyyar Aure

A yau shafin namu zai zo muku da tsarabar yan mata masu shirin zama Amaren bayan sallah.

 Daga cikin abubuwan da suke sa ango ko maigida ya ji ba ya sha’awarki ko kuma ko da yana sha’awar taki amma sai ki ga ya rage, haka nan ke ma ki ji ba ki sha’awarsa ko kwadayinsa ya ragu a wurinki, akwai rashin samun wadatacciyar ni’ima.

 Abin da mata suka kasa bambancewa da jikinsu shi ne a tunanin mace mafi yawanci duk mace da ke da jiki mai kyau tana da ni’ima, duk mace mai damshi tana da ni’im a’a wannan ba haka ba ne. Kirar ki daban ni’imar jikin ki daban bai zama lallai idan kina da damshi ya zama lallai kina da dumi ba danshi daban ni’ima daban.

Amma dole ki san jikinki, ki karanci yanayin jikinki kamar littafi domin babu wanda ya sanki fiye da ke kanki!

 Matukar yawan ni’imar jikinki ya sauka dole ki ga sauyi, babban maganin wannan matsala ita ce:

 1.Ki nisanci sanyi. 2. Ki nisanci abu mai yawan kitse, 3. Ki nisanci yawo kafa ba takalmi da zama a kan tantagaryar siminti ko tayis 4. Idan so samu ne ruwan tsarkinki kar ya zama mai sanyi. 5. Ki nisanci abubuwa masu matsanancin zaki.

  1. In so samu ne, ki mayar da kayan ganye su zama abincinki. 7. Ki mayar da ‘ya’yan itatuwa su zama ruwan shanki. 8. Ki koyi miyar ganye domin tana ba da ma’ana. 9. Ki mayar da kankana ta zama abokiyar hirarki.
  2. Ki mayar da kifi ya maye gurbin nama. 11. Hanta da koda da zuciya, su zama su ne namanki, ke kanki za ki ji bambanci.

Gyaran Jiki:

Ki sami ganyen Magarya da lalle ki dafa in ya dan huce sai ki shiga, in kin fito ki yi tsumin da kanunfari na kwana uku sai ki nemi garin hulba, habbatussauda, alkama, gyada, ridi danyar shinkafa, sai ki hade su a wuri guda ki nike sai ki dinga yin kunu kina sha da nonon rakumi ko madara ko nonon shanu za ki sha da awa biyu kafin ki yi bacci da kuma awa biyu bayan kin ci abinci da safe kuma idan za ki kwanta ki shafa man hulba a mamanki. Wannan hadin in kina sha yana gyara fata, kuma yana kara ni’ima.

Bushewar Gaba

 Domin magance wannan matsala, kina iya samun kwai daya, ki fasa shi sannan ki kada ya kadu sosai sai ki sami ganyen Ugu ki matse ruwansa kamar rabin kofi, ki juye a kan ruwan kwan da kika fasa sai kuma ki saka zuma, cokali uku ki kada su sosai, ki zuba madarar gari cokali biyu ki ci gaba da kadawa sosai sai ki kara zuba lemun tsami bari daya don ki rage karnin kwan, ki kuma bugawa sai ki shanye idan kika yi na kwana uku a jere duk bushewar gabanki sai ni’ima ta tsattsafo.

People are also reading