NSCDC a Kano ta Damke Masu Addabar Al'ummar Jihar da Sace Sace
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Rundunar tsaron fafaren hula (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da barnatar wayoyin fitilun kan titi a yankin karamar hukumar Fagge.
Wadanda aka kama sun hada da wani Adnan Umar, mai shekara 26, da Musa Shu’aibu, mai shekara 24, kamar yadda kwamandan hukumar Mohammad Lawal-Falala ya bayyana.
Vanguard News ta wallafa cewa kwamandan, Mohammad Lawal-Falala ta cikin sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi ya bayyana fitar ya ce an kama bata-garin ne da tsakar dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NSCDC a Kano ta bayyana cafke wasu matasa uku da zargin satar babur da suka hada da wani Saminu Magaji, Haruna Idris da Ahmad Abubakar.
Daily Trust ta wallafa cewa dukkanin matasan mazauna Gwammaja ne da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano.
Hukumar NSCDC ta karada cewa baya ga satar babur, ana zargin matasan sun dade suna haurawa gidajen jama'a su sace babura da sauran kayan amfani.
Yanzu haka dai kwamanda Mohammad Lawal-Falala ya ce ana zurfafa bincike kan matasan biyar da aka kama, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an gama.
A wani labarin kun ji cewa hukumar tsaron fararen hula ta kasa (NSCDC) a jihar Kano ta damke wasu da ake zargi da safarar mutane zuwa kasashen ketare.
Hukumar ta bayyana cewa an ceto wasu mutane 14 da ake niyyar fita da su zuwa kasar Kamaru ta iyakar Maidguri domin ci rani.
Asali: Legit.ng