Home Back

Saurayi Da Budurwarsa Sun Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa A Kano

leadership.ng 2024/7/1
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Wata kotun shari’ar Musulunci ta tsare wata budurwa da saurayinta a gidan yari kan zargin sace kayan lefen ’yar uwarsa a Jihar Kano.

An gurfanar da saurayin da budurwarsa ne kan zargin sata da kuma karbar kayan sata a gaban Kotun Musulunci da ke zamanta a unguwar Rijiyar Lemo a jihar.

Bayan jami’i mai gabatar da kara, Usman Idris Shu’aibu Dala, ya karanto takardar tuhumar, saurayin ya amsa laifin da ake zarginsa.

Amma ita budurwar ta shaida wa alkali cewa biyu daga cikin kayan lefen da ake zargi kawai saurayin nata ya kawo mata, kuma ta mika su ga kotu.

Bayan sauraren su, alkalin kotun, Khadi Danbaba, ya bayar da umarnin tsare su a gidan yari zuwa ranar Larabar nan.

Ya kuma bayar da umarnin zuwa da iyayensu a zaman kotun da za a ci gaba ranar Laraba.

People are also reading