Home Back

Dakarun Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 220, Sun Kwamuso Wasu Sama da 300 a Najeriya

legit.ng 2024/6/29
  • Dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da kai samame kan ƴan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar nan
  • Hedkwatar tsaro (DHQ) ta ce sakamakon haka sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 220, sun kamo wasu 395 tare da ceto mutanen da aka sace
  • Kakakin DHQ, Manjo Janar Buba ya ce sun kuma kwato mugayen makamai daga hannun waɗanda ake zargin duk a makon jiya kaɗai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar murƙushe ƴan ta'adda 220 a sassa daban-daban na ƙasar nan cikin mako ɗaya da ya gabata.

Dakarun sojojin sun kuma damke wasu ƴan ta'adda da masu aikata miyagun laifuka 395 tare da ceto mutane 202 da aka yi garkuwa da su.

Sojojin Najeriya.
Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a makon jiya a Najeriya Hoto: Nigerian Army Asali: Twitter

Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro (DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a 21 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa sojojin sun karɓe lita 1,099,860 na danyen mai da aka sace tare da kama barayin mai 55 duk a cikin makon jiya, The Nation ta ruwaito.

Sojoji sun kwace manyan makamai

Janar Buba ya ce sojojin sun kwato makamai 432 da suka hada da bindigogin PKT guda uku, G3 daya, AK47 guda 83, bindigar gida 18, da wasu bindigogi 16.

Ya ce sojojin sun kuma kwato alburusai 9,004 a ayyuka daban-daban da suka gudanar a sassan ƙasar nan cikin kwanaki bakwai, cewar rahoton Vanguard.

Sauran kayayyakin da aka kwato a cewar kakakin DHQ sun hada da rediyon baofeng guda uku, motoci takwas, babura 32, wayoyin hannu 59 da kuma kudi N813,550.00.

Sojoji sun ruguza ɓarayin mai

Janar Buba ya ce sojojin yankin Neja Delta sun kwace man dizal lita 1,101,700 da aka tace ta haramtacciyar hanya tare da lita 27350 na kalanzir da kuma lita 150 na man fetur. 

"Sojojin sun bankaɗo tare da lalata wuraren tace mai na haram guda 105, rijiyoyi 51, kwale-kwale 38 da tankunan ajiya 51," in ji shi.

Mahara sun ɗauke basarake a Nasarawa

Kuna da labarin cewa mahara sun yi garkuwa da wani mai riƙe da sarauta, Madakin Shabu Musa Shu'aibu jim kaɗan bayan ya fito daga masallaci a Nasarawa.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Rahman Nansel ya ce tuni dakarun ƴan sanda suka bazama domin ceto mutumin.

Asali: Legit.ng

People are also reading