Home Back

ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA: Ma’aikatan Kano sun nemi Tinubu ya watsar da shawarwarin IMF da Bankin Duniya

premiumtimesng.com 2024/4/28
ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA: Ma’aikatan Kano sun nemi Tinubu ya watsar da shawarwarin IMF da Bankin Duniya

Masu zanga-zanga a Kano sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya watsar da bin tafarkin tsarin harkokin kuɗaɗen da ƙasashen Turai, musamman Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya suka ɗora Najeriya a kai.

Shugaban NLC na Jihar Kano, Kabiru Inuwa, ya danganta raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da ake fuskanta a Najeriya, cewa sun faru ne saboda aron tsarin tattalin arzikin Turai na Najeriya ta yi.

Inuwa, wanda ya jagoranci zanga-zanga a Kano, daga Filin Sukuwa, a cikin tsatstsauran matakan tsaro, ya gabatar da jawabi ga gwamnatin jihar Kano, a ƙofar Gidan Gwamnati.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi ne ya tarbe su a gidan gwamnati.

Inuwa ya ce masifar tsadar kayan abinci, kayan masarufi da sauran kayan amfanin yau da kullum, har ma da yawaitar miliyoyin mutanen da ke fama da fatara da talauci, duk hakan ya faru ne daga tsarin tasarifin kuɗaɗen da ake kwaikwayo daga Turai.

“Su da manyan bankuna da cibiyoyin bada ramcen kuɗaɗe na duniya, ba za su iya ba ƙasa ramce ba tare da sun gindaya mata tsauraran sharuɗɗa ba.

“Daga cikin sharuɗɗan akwai inda ake cewa ya zama tilas ƙasar da za ta karɓi ramcen ta janye duk wani tallafi da ta ke wa talakawa da masara galihu. Saboda me? Saboda su na so ƙasar ku ta afka cikin ruɗanin yaƙi tsadar rayuwa da ɓalɓalcewa.

“Irin yadda fatara da talauci ke ƙara hauhawa a kowace rana, abin tsaro ne. A kullum farashin kayan abinci sai tashi suke yi.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa muke ƙorafi. Saboda haka a ƙyale mu mu yi numfashin samun sauƙin rayuwa. Su yi watsi da shawarwarin IMF da Bankin Duniya, duk ingaza mai kantu ruwa ne su ke yi mana.

“Shawarwarin IMF da Bankin Duniya ba na ƙwarai ba ne, ba su da tasiri da alfanu a ƙasashen Afrika. Saboda mayunwaci ai hasalallen mutum ne.”

An Tashi Zanga-zangar Jigawa Ba Kyakkyawan Shiri A Dutse:

A maƙauciyar Jihar Kano kuma, wato Jigawa, an watse kafin tashi zanga-zanga, saboda ba a tsara ta a natse ba, kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu labari.

An fara zanga-zanga daga Filin Idi na Dutse, aka ƙarƙare Sakateriyar NLC a kan titin bai-fas na Ibrahim Aliyu, ƙasa da kilomita biyu daga inda aka fara zanga-zangar.

Masu zanga-zanga sun watse saboda sun ji an ce ba za a ƙarasa Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa ba. An ce hakan ya faru, saboda Gwamna Umar Namadi ba ya gari.

 
People are also reading