Home Back

Messi Ya Magantu Kan Ritaya a Kwallon Kafa, Ya Fadi Kungiyarsa Ta Ƙarshe

legit.ng 2024/10/5
  • Lionel Messi ya magantu kan kungiyar kwallon kafa da zai yi ritaya bayan shahara da ya yi a fagen buga tambola
  • Messi ya tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami ita za ta kasance kungiyarsa ta karshe a kwallon kafa
  • Fitaccen ɗan wasan mai shekaru 36 ya bayyana haka ne a jiya Laraba 12 ga watan Yuni yayin hira da ESPN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Miami, Amurka - Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa a duniya, Lionel Messi ya bayyana kungiyar da zai ajiye tambola.

Messi ya ce zai yi ritaya ne a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami da ke buga gasar 'Major League Soccer' a kasar Amurka.

Fitaccen ɗan wasan mai shekaru 36 ya bayyana haka ne yayin hira da ESPN a jiya Laraba 12 ga watan Yuni.

"Ina tunanin Inter Miami za ta zamo kungiyar ƙwallon ƙafa ta karshe da zan buga wasa."
"Na shafe shekaru ina buga wasa, ina kaunar buga kwallon kafa, ina jin dadin harkar kwallon kafa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Amma abin takaici ne duka wanann zai zo karshe, abu ne mai matukar wahala barin Nahiyar Turai zuwa nan Miami."

- Lionel Messi

Tun bayan bayyanarsa a fagen kwallon kafa a 2004, Messi ya buga kwallo ne a ƙungiyoyin kwallon kafa uku kadai a rayuwarsa.

Kungiyoyin sun hada da Barcelona da ke Spain da PSG a kasar France da kuma Inter Miami da ke Amurka.

Mbappe ya koma kungiyar Real Madrid

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen dan wasan gaba na France, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid da buga wasa.

Dan wasan ya sanya hannu a duka takardun yarjejeniya da kungiyar domin fara wasa a sabuwar kaka mai zuwa.

Madrid ta dade tana zawarcin dan wasan shekaru da dama kafin samun nasarar dauke shi daga kungiyar PSG.

Asali: Legit.ng

People are also reading