Home Back

Mahara sun kashe gomman mutane a gabashin Kwango

dw.com 2024/7/3
Dakarun sojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango a birnin Goma
Dakarun sojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango a birnin Goma

Wasu shugabannin yankin sun tabbatar da cewa, mayakan CODECO ne suka kai hare-hare a yankin Djugu a ranakun Alhamis da kuma Juma'ar da suka gabata.

Shugaban yankin Djugu, Vital Tungulo ya ce yawancin mutanen an kashe su ne ta hanyar daba musu adda, yayin da wadanda suka yi yunkurin guduwa aka harbe su. Kana maharan sun kone gidajen jama'a da dama tare da kwasar ganima. Kawo yanzu, mazauna yankin na cewa, an birne wadanda suka riga mu gidan gaskiyar a rami guda a kauyen Gangala.

Karin bayani: An kashe rayuka a gabashin kasar Kwango 

Tun a farkon wannan shekarar ce, lamura suka kara rincabewa sakamakon zafafa kai hare-hare da kungiyar ke yi. Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Kwango ta dora alhakin yawancin kisan fararen hula kan kungiyoyin CODECO da kuma ADF.

People are also reading