Sallah: Atiku Ya Kai Ziyara Ga IBB da Janar Abdulsalami a Minna, Hotuna Sun Bayyana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ziyarar Barka da Sallah.
Haka nna kuma Wazirin Adamawa ya wuce ya kai gaisuwar Barka da Sallah ga tsohon shugaban ƙasa, Abdullsalami Abubakar.
Atiku Abubakar ya kai wa waɗannan tsofaffin shugabannin ziyara ne har gidajen su da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ya tabbatar da haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba.
Atiku ya kuma wallafa hotunan ziyarar da ya kai wa jiga-jigan biyu domin taya su murnar bikin Babbar Sallah wadda aka yi ranar Lahadin da ta gabata.
"A yau na samu kai ziyarar barka da Sallah ga tsofaffin shugabanni, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) da Janar Abdulsalami Abubakar a gidajensu da ke Minna a jihar Neja."
Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 da ya gabata.
Sai dai ya sha ƙasa a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a zaɓen wanda aka kai ruwa rana tsakanin manyan ƴan takara uku.
A wani rahoton na daban Mambobin babbar jam'iyyar adawa PDP sama da 4,000 sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benuwai.
Gwamna Hyacinth Alia ne ya karɓe su da kansa a wani taro da aka shirya lokacin da yake zagayen godiya ga al'ummar jihar da suka zaɓe shi.
Asali: Legit.ng