Gwamnatin Soja Ta Burkina Faso Ta Dakatar da BBC da VOA Daga Kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Burkina Faso sun dakatar da gidajen rediyon BBC da Muryar Amurka daga gudanar da shirye-shirye a kasar.
Dakatarwar ta biyo bayan yada rahoton da gidajen rediyon suka yi ne a kan harin da ake zargin sojojin da kaiwa kan fararen hula.
A wani rahoton da jaridar Al-Jazeera ta fitar ya nuna cewa sojojin sun kashe akalla mutane 223 ciki harda yara 56.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Alhamis ne dai hukumar sadarwar kasar ta sanar da dakatar da manyan gidajen rediyon na sati biyu, cewar jaridar Reuters
A cewar sanarwar da sojojin suka fitar, an dakatar da gidajen rediyon ne saboda cin fiska ga kasar wurin ruwaito cewa sojojin sun ci zarafin fararen hula.
Sojojin sun ce labarin ba shi da inganci kuma gidajen rediyon sun yi gaggawa wurin rashin tuntubar gwmantin domin jin gaskiyar lamarin.
A wani rahoton kuma, ku ji cewa sojin da ke mulki a Burkina Faso sun sanar da yunkurin juyin mulki da wasu sojoji su ka yi
Sojin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa inda su ka ce an kama sojoji hudu kan zargin cin amanar kasa
Asali: Legit.ng