Home Back

Gwamnan Kano ya umarci jami’an tsaro su cafke duk wanda ya fito zanga-zanga

dalafmkano.com 2024/6/25

Gwamnatin jihar Kano ta umarci jami’an tsaron ƴan sanda, da na DSS, da rundunar tsaro ta Civil Defense, da su cafke dukkanin mutanen da suka fito gudanar da zanga-zanga a faɗin jihar Kano.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwar da babban daraktan yaɗa labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Laraba.

Ya ce sun samu bayanan sirri kan wasu maƙiya Kano na yunƙurin haɗa zanga-zanga da sunan nuna goyon bayan su ga Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, lamarin da gwamnatin ba zata aminta da shi ba.

Ya ce gwamnatin jihar ta haramta dukkanin wata zanga-zanga ta kowacce fanni a faɗin jihar Kano, inda ya ce duk wanda aka kama da laifin Zanga-zangar za’a ɗauki tsattsauran matakin kai mutum kotu, domin girbar abinda ya shuka.

Wannan dai na zuwa ne yayin da dambarwar rushe sarakuna biyar a faɗin jihar Kano, ke ci gaba da ɗauki sabon salo, tun bayan da majalisar dokokin jihar ta rushe masaratun biyar bayan da ta yiwa dokar kafa masarautun kwaskwarima, wanda gwamnan Kano ya bayyana Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarki.

People are also reading