Home Back

Rikicin Masarautar Kano: NNPP Ta Nesanta Kanta Daga Umarnin Kwankwaso Ga Ƴan Majalisa

leadership.ng 2024/10/6
Rikicin Masarautar Kano: NNPP Ta Nesanta Kanta Daga Umarnin Kwankwaso Ga Ƴan Majalisa 

Shugabancin jam’iyyar NNPP na ƙasa ya nisanta kansa daga umurnin da jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayar ga ƴan majalisar tarayya. Kwankwaso, a wata wasika mai ɗauke da sa hannun Dr. Ajuji Ahmed, ya umurci ƴan jam’iyyar NNPP a majalisar dokokin ƙasar nan da su soki shugaba Bola Tinubu da gwamnatin tarayya kan rikicin masarautar Kano.

A wata wasiƙa da suka aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, shugabancin jam’iyyar NNPP wanda shugaban jam’iyyar na kasa Agbo Gilbert Major da sakataren jam’iyar Kwamared Oginni Olaposi Sunday suka wakilta, sun bayyana cewa umarnin Kwankwaso ba ya wakiltar jam’iyyar ta su.

Sun bayyana cewa matsayar jam’iyyar ta karkata ne ga ci gaba da jin dadin ƴan Nijeriya, kuma rikicin masarautar Kano lamari ne da ya ke kotuna, inda suka buƙaci majalisar dokokin da kada ta tsoma baki.

Jam’iyyar NNPP ta jaddada buƙatar taka-tsan-tsan da kuma inganta tsaro a Jihar Kano domin daƙile taɓarɓarewar doka da oda, inda ta bayyana cewa jam’iyyar ba ta son shiga rikici da hukumomin tarayya musamman hukumomin tsaro.

Don haka suka buƙaci majalisar dokokin da ta yi watsi da duk wani umarni da Dr. Ajuji Ahmed ya bayar kan wannan batu.

People are also reading