Home Back

Tinubu ya naɗa Akintunde Sawyer Shugaban NELFUND, Hukumar Bada Ramce ga Ɗalibai

premiumtimesng.com 2024/5/12
Tinubu ya naɗa Akintunde Sawyer  Shugaban NELFUND, Hukumar Bada Ramce ga Ɗalibai

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗa shugabannin Hukumar Bada Lamuni ga Ɗaliban gaba da Sakandare, NELFUND.

Tinubu ya amince da naɗa Akintunde Sawyerr a matsayin Manajan Darakta, kuma Shugaban Hukuma.

Sai kuma Frederick Oluwafemi Akinfala, wanda aka naɗa Babban Daraktan Harkokin Kuɗi da Gudanarwa.

Mustapha Iyal shi aka naɗa Babban Daraktan Ayyuka na NELFUND, kamar yadda sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar mai ɗauke da sa hannun sa a ranar Juma’a.

PREMIUM TIMES ta buga labarin gyare-gyaren da Shugaban Ƙasa ya yi wa tsare-tsaren hukumar ta NELFUND a ranar Juma’a, waɗanda a cikin su akwai wasu sharuɗɗa 8 da ke tattare da Lamunin Kuɗin Karatun Ɗaliban Gaba Da Sakandare.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sa wa dokar kafa Hukumar Bada Lamuni ga Ɗaliban Manyan Makarantu hannu, bayan an yi wa dokar gyare-gyaren da suka wajaba.

Cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu, wadda ke ɗauke da sa hannun Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, an bayyana gyare-gyaren da aka yi wa dokokin, waɗanda suka haɗa da:

1. Duk wanda ya bayar da bayanan ƙarya wajen cika fam ɗin neman lamunin gwamnatin tarayya, to ya aikata laifin cin amanar ƙasa, kuma hukuncin ɗaurin shekaru 3 a gidan kurkuku zai hau kan sa.

2. Hukumar Bada Bashi ga Ɗalibai (NELFUND), za ta iya yafe bashi ga ɗalibin da rai ya yi halin sa bayan ya karɓi bashin. Ba za a tilasta iyayen sa su biya ba.

3. Ɗalibin da aka bai wa ramcen zai iya neman a ƙara masa wa’adin lokacin biyan kuɗin, matsawar ya je kotu ya karɓo kwafen rantsuwar cewa har yanzu bai samu aikin da ya fara samun kuɗi ba, tun bayan kammala aikin NYSC da ya yi.

4. NELFUND za ta fara neman ɗalibi ya biya kuɗin da ya karɓa bayan shekaru biyu da kammala NYSC.

5. Idan ɗalibi ya nemi ramcen kuɗin da zai biya kuɗin karatu, to NALFUND za ta biya kuɗin a sasusun banki na makarantar ne. Amma idan ramcen kuɗin ɗawainiyar faɗi-tashin karatun sa ne, to a na sa asusun bankin za a tura masa.

6. Ba za a hana ɗalibi ramcen ba, ko da kuwa gwamnatin tarayya ta na bin mahaifin sa bashi.

7. An cire sharaɗin sai ɗalibi ya bada sunan mutumin da zai tsaya masa a wurin karɓar bashin. Muddin aka tantance shi, za a ba shi lamunin kawai.

8. An cire sharaɗin sai hukuma ta ɗan adadin ƙarfin arziki ko ƙarfin talaucin iyayen ɗalibi kafin a ba shi ramcen.

People are also reading