Home Back

Ko Gwamnatin Tarayya Za Ta Iya Ceto Kananan Hukumomi Daga Gwamnoni?

leadership.ng 2024/7/3
Ko Gwamnatin Tarayya Za Ta Iya Ceto Kananan Hukumomi Daga Gwamnoni?

A wani yunkuri na ceto kananan hukumomi daga dabaibayin gwamnoni, gwamnatin tarayya ta maka daukacin gwamnonin kasar nan 36 a gaban kotun koli na neman a sakar wa kananan hukumomi mara su ci gashin kansu.

Karamar hukuma ita ce gwamnati mafi kusa da jama’a, kuma ita ke bunkasa al’umma a matakin farko. Sai dai kuma, ingantaccen shugabanci a kananan hukumomi ya gamu da cikas sakamakon irin dabaibayin da gwamnonin jihohi ke musu.

Kudaden kananan hukumomi a asusun tarayya da ake biya duk wata suna zuwa ne daga gwamnatocin jihohinsu.

A cikin karar mai lamba SC/CB/343/2024, da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, ya shigar, gwamnatin tarayya tana neman a bai wa kananan hukumomi cikkiyar ‘yan ci a kasan a matsinsu na mataki na uku na gwamnati.

Ta kuma bukaci kotun kolin da ta bayar da umarni tare da haramta wa gwamnonin jihohi rusa shugabannin kananan hukumomin da aka zaba ba da kuma bayar da umarnin bayan kudaden kananan hukumomi kai tsaye ga asusunsu daidai da yadda kundin tsarin mulki ya tanada ba a asusun hadin gwiwa ba da gwamnoni suka kirkira ba bisa ka’ida ba.

A karar da gwamnatin tarayya ta shigar, gwamnatin tarayya na bukatar kotun koli ta bayar da umarni na dakatar da gwamnonin ci gaba da kafa kwamitocin rikon kwarya da za su tafiyar da al’amuran kananan hukumomi wanda ya saba wa tsarin mulkin dimokuradiyya da aka amince da shi.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa Nijeriya a matsayinta ta tarayya, ita ce ta kirkiro kundin tsarin mulki na 1999, wadda aka yi wa kwaskwarima, inda shugaban kasa, a matsayinsa na shugaban gwamnatin tarayya, ya rantse da cewa zai tabbatar da bin tsarin kundin mulki.

Tun bayan zuwan mulkin dimokuradiyya a kasar nan a shekarar 1999, gwamnatocin jihohi ke dabaibaye kananan hukumomi 774 da ke kasar nan.

Ba wai kawai gwamnoni na zabar makusantansu da za su gudanar da harkokin kananan hukumomi ba, har ma suna zayyana yadda za a kashe kudadensu, musamman kason da ake samu daga asusun tarayya.

Wannan lamari yana gunana ne a tsakanin jam’iyyun siyasa masu mulkin gwamnatocin jihohi karkashin kwamishinonin kananan hukumomi da al’amuran sarauta.

Wannan lamari ya sa kananan hukumomi sun rasa ‘yancin kai na gudanar da harkokin kudade da kuma ‘yancin gudanar da ayyuka, wanda ya mayar da su baya da kuma kasa samar da muhimman ayyukan da al’umm za su amfana.

Duk wani yunkuri na bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ta hanyar gyaran kundin tsarin mulkin kasa, gwamnonin sun toshe.

Hatta kotuna da dama, ciki har da kotun koli, sun yi kokarin shiga tsakani a lokuta da dama kan yadda gwamnonin ke nuna halin ko-in-kula da kananan hukumomi ke yi ba tare da cimma wata nasara ba.

Ba wai kawai ba a gudanar da zabuka ba ne ko kuma ana yawan cire shugabanni kananan hukumomi da kansiloli kadai, ana yawan kafa kwamitocin riko domin gudanar da harkokin kananan hukumomi duk saboda kudaden shiga da suke samu.

A yayin da ake ci gaba da sauraren karar a makon da ya gabata, kwamitin alkalai guda bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin mai shari’a Garba Lawal, ya umarci gwamnonin wanda babban lauyoyin jihohi suka wakilta da su gabatar da takardar kariyarsu ga wannan sammacin cikin kwanaki bakwai. An dai dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yunin 2024.

Abin jira a gani dai shi ne, yadda gwamnatin tarayya za ta bi sawun karar a lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci ko dai ta samu nasara ko akashin haka.

People are also reading