Home Back

CSO Ta Wanke Ganduje Daga Zargin Rashawa, Ta Kalubalanci Gwamnatin Kano

legit.ng 2024/6/2
  • An wanke shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa na cin hanci da rashawa
  • Gamayyar kungiyoyin Gaskiya da Adalci ta bayyana cewa an saka son rai da kiyayya a tuhumar da ake yi wa Ganduje
  • Kungiyar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da bangaren adawa da Ganduje ke yi, da cewar adawa ce ga kujerarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An wanke shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje daga zargin karbar cin hanci da rashawa.

Gamayyar kungiyoyin Gaskiya da Adalci ta bayyana haka a rahotonta na farko kan binciken tsohon gwamnan Kano.

Kugiya ta wanke Ganduje daga zargin rashawa.
Kungiya ta zargi gwamnatin Kano da laifin tuhumar Ganduje ba tare da hujjoji ba. Hoto: CTJ, Abdullahi Umar Ganduje. Asali: UGC

A cikin rahoton mai dauke da sa hannun shugabanta, Dr Okwa Dan, kungiyar ta ce an yi nufin bata sunan Ganduje ne aka bullo da tuhume-tuhumen, in ji jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gamayyar ta kara da cewa, hujjojin da aka gabatar wa kotu na karbar cin hanci da rashawa ba su da wata alaka ta nesa ko ta kusa da Ganduje.

Ta yi gargadi kan amfani da madafun iko da kuma karfin gwamnati wajen farautar abokan hamayyar siyasa.

Kungiyar ta zargi gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf, tare da abokin hamayyar Ganduje kuma tsohon ubangidansa, Rabiu Kwankwaso, kan abin da suka kira 'bata suna.'

Zargin Ganduje ya karbi cin hanci

Mista Dan ya kuma ce faifan bidiyo da aka ce ya nuna tsohon gwamnan ya na karbar daloli na rashawa yana sokewa a aljihu na boge ne wanda aka kirkire shi domin batanci.

Ya ce bidiyon karbar Dala ba shi da "sahihanci " wanda ya sa kungiyar ta yi fatali da shi a matsayin hujja abar kamawa kan zargin tsohon gwamnan.

Shugaban kungiyar ya karkare da cewa:

“Gamayyar kungiyoyin Gaskiya da Adalci tana so ta bayyana a fili cewa Dr Umar Ganduje bai aikata wani laifi ba a lokacin da yake kan mulki sabanin yadda suke kokarin bata shi a idon jama'a."

Gwamnatin Kano na kokarin bata Ganduje

Wata kungiyar siyasa ta zamantakewa a Kano, Concerned Forum, ta ce harin bata suna da abokan hamayya ke kaiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa ba zai yi tasiri ba.

Da yake zantawa da jaridar Leadership a Kano, sakataren kungiyar Kwamared Auwal Shu’aibu, ya zargi gwamnatin jihar Kano da kokarin kunyata Ganduje a idon duniya.

APC: An nemi kotu ta tsige Ganduje

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kano bai kare ba, yayin da wani jigo a jam’iyyar ya maka Abdullahi Ganduje a kotu.

Mohammed Saidu-Etsu ya bukaci Ganduje da ya sauka daga kujerar shugaban APC, sannan ya nemi kotun da ta bayyana nadin na tsohon gwamnan Kano a matsayin 'haramtacce'.

Asali: Legit.ng

People are also reading