Home Back

Amurka da Pilippines na atisayen soji a tekun kudancin China

dw.com 2024/5/19
Amurka da Pilippines na atisayin sojin a tekun kudancin China
Amurka da Pilippines na atisayin sojin a tekun kudancin China

Fiye da sojoji 16,700 ke halartar wannan kasaitacen atisayen jiragen ruwan yaki da na sojojin kasa wanda za a kammala a ranar 10 ga wannan wata na Mayu a yankin da ake samun tashe-tashen hankula tun bayan da China ta bayyana wani bangare a matsayin mallakinta.

A makon da ya gabata kasar Philippines ta zargi jami'an tsaron gabar tekun China da harbin wasu jiragen ruwanta guda biyu da igiyar ruwa tare da toshe masu hanyar shiga wani yanki na tekun kudancin Chinar da kasashen biyu ke takaddama a kansa.

Karin bayani: Chaina ta jaddada kudirinta na hade Taiwan

Ana dai fargabar wannan yanayi ya rikide zuwa babban rikici a yankin tsakanin China da Amurka da ke da yarjejeniyar tsaro da Philippines a dadai kuma lokacin da Beijing ke kara matsa lamaba ga tsibirin Taiwan wanda shima ke dasawa da Washigton.

People are also reading